Labarai

Ta cire jiji da kai Na mata ta Fara Yi Masa Magana A Instagram yanzu Gashi har sunyi Aure

Wata Budurwa ta shelanta cewar da kanta ta fara yiwa matashin magana a Kafar Instagram shekaru biyar baya da suka wuce, yanzu gashi har an daura musu Auren sunnah.Kamar yadda shafin dimokuraɗiyyar na ruwaito

Ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram tare da hotunan daurin Auren ta ita da Mijin nata, kuma a dukkan alamu Aure ne na Soyayyah, kuma mai cike da alfahari.Ta cire jiji da kai Na mata ta Fara Yi Masa Magana A Instagram yanzu Gashi har sunyi Aure

Wallafar bata bayyana cikakken sunan Budurwar ba sai dai an saka (Mrs. Adda_Tee).

Wannan na zuwa ne bayan da Malamai suke kara wayar da kan al’umma musamman mata kan cewa mace zata iya bayyana soyayyar ta ga Namijin da take so Mai Kamala da mutunci ko kuma Mahaifin yarinya zai iya samarwa yarinya miji da kan sa ba tare da yaji na’uyin hakan ba.

 

Sai dai har yanzu mata da al’adar arewaci suna ganin zubar da mutuncin mace ne ta gayawa Namiji tana son sa da sunan Aure, suna tunanin hakan zai iya jawo rai ni da zubar da girma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button