Labarai

Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye – Bincike

Matan da ba sa cin nama za su iya fuskantar yiwuwar karyewa a kwankwaso nan gaba a rayuwa, kamar yadda wani bincike ya nuna. BBCHausa na ruwaito

Masu binciken sun rika bin rayuwar mata   26,000 na tsawon shekaru 20 kuma sun gano cewa  kashi daya bisa uku na matan da ke cikin rukuni da ba sa cin nama sai  kayan lambu ko kayan itace za su iya samun karaya ko targade fiye da masu cin nama.

Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye - Bincike
Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye – Bincike

Kwararru daga Jami’ar Leeds sun ce wasu daga cikin matan da ba sa cin naman na iya rasa sinadaran inganta lafiyar kashi  da tsokar kashi lamarin da ke haifar da hadarin karaya.

Sai dai duk da haka mawallafan rahoton sun ce bai kamata wadanda ba sa cin nama su yi watsi da cin kayan lambu da na itace ba.

Masu binciken sun yi nazari  a kan rukunin mata masu shekaru 35 zuwa 69 domin tantance alaka tsakanin lafiya da abinci.

Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye - Bincike
Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye – Bincike

Kusan kashi 28 cikin 100 na matan da aka rika bin yadda suke rayuwa  wadanda ba sa cin nama ne, yayin da kashi daya cikin dari wadanda ba sa cin nama ne da madara da kwai da duk wani nau’in abinci da ake samu daga wurin dabobbi.

Jagoran binciken, James Webster, ya ce: “Bincikenmu ya nuna damuwa a kan hadarin samun karaya  ga matan da ba sa cin nama.

“Sai dai duk da haka kamar yadda yake game da kowane abinci, yana da muhimanci a fahimci yanayin mutum da kuma abinci mai gina jiki da ake bukata domin inganta lafiyar jiki.”

Mista Webster ya ce kayan lambu da na itace ba sa samar da abinci mai gina jiki irin su sinadarin Protein da Calcuim wadanda aka fi samunsu a nama fiye da ganyayyaki.

“Rashin samun wadannan abubuwan gina jiki zai iya samar da kashi mara kwari kuma yana shafar ingancin tsokar kashi wanda zai iya sa mutum cikin hadarin samun karaya a kugu,” in ji shi.

Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye - Bincike
Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye – Bincike

Sai dai Mista Webster ya ce rashin cin nama ya bambanta daga mutum zuwa mutum kuma zai iya “inganta lafiya ko akasin haka”, kamar sauran abinci da ake samu daga dabbobi.

Su ma sauran masana kimiyya da ke cikin aikin sun ce mata za su iya kula da lafiyar kashi ta hanyar ganin cewa sun yi kokarin kaucewa rama, tare da cin abinci mai dauke da sinadarin B12 tare kuma da motsa jiki a-kai-a-kai.

Dr Darren Greenwood ya ce “Wannan bincike wani bangare ne da ke nuni da yadda mata suke rayuwa idan tsufa da kuma abinci mai gina jiki da suke ci da lafiyar kashi da kuma tsokar kashi.

“Ana bukatar karin bincike domin sanin rawar da nauyin jiki ya ke takawa tare da gano dalilan da ke janyo haka a masu cin nama da masu cin kayan lambu da na itace.

Ita ma Farfesa Janet Cade wadda tana cikin mawallafan rahoton ta ce binciken “na da muhimanci saboda zai bada damar fahimtar hadarin da ke tattare da masu cin kayan lambu na tsawon lokaci da kuma matakan da ya kamata a dauka domin kaucema haka.”

Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye - Bincike
Rashin cin nama ga ƴa mace na iya sa Kwankwasonta ya karye – Bincike

Masu binciken sun ce akwai bukatar gudanar da karin bincike domin tantance ko za a iya samun sakamako makamancin wannan tsakanin maza.

Please share 🙏

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button