Kannywood

Na Yi Mafarki Fati Washa Ta Riƙe Hannuna Mun Shiga #Aljanna cewar Sabon Jarumin Kannywood Zeek Ilela

Sabon jurumi a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Auwal Abdullahi Zeek Ilela ya bayyana cewa wata rana ya yi mafarki jaruma Fati Washa ta riƙe hannunsa sun shiga #Aljanna a L@hira. Shafin Bashir Abdullahi na ruwaito

Jarumi Auwal ya ƙara da cewa wannan shi ne babban dalilinsa na shiga harkar fina-finan Hausa saboda ya tabbatar akwai alkhairi a cikin mafarkin tunda ya haɗu da Fati Washa.Na Yi Mafarki Fati Washa Ta Riƙe Hannuna Mun Shiga #Aljanna, Inji Sabon Jarumin Kannywood Zeek Ilela

Na daɗe ina son Fati Washa domin mace ce mai ƙira da cikar halittar macentaka, wata rana na yi mafarki mun haɗu da ita a lahira, ga ƴan uwana da abokaina da sauran mutane amma ita ce ta kama hannuna mu ka shiga gidan aljannah tare, shi isa na yi sauri na shiga cikin harkar fim domin mu haɗu tare tun a duniya tayadda mafarkina zai zama gaskiya a ranar lahira,”. Inji shi.

Auwal Abdullahi ya cigaba da cewa bai san haka ƴan fim su ke da kirki ba sai da ya shiga cikinsu saboda haka mutane su na yi musu gurguwar fahimta ne a rayuwa ta zahiri amma a baɗili su ɗin mutanen kirki ne, “a daina yi wa ƴan fim mummunar fassara domin mutanen kirki ne,”. Inji Sabon Jarumin na Kannywood Zeek Ilela.

Me za ku ce?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button