Mata Ta Kama Mijinta Yana Lalata da ‘Yarsu Me Shekara 14
Dubun wani mutum a jihar Katsina ta cika bayan da matar sa ta damke shi dumu-dumu ya na aikata fasikanci da ‘yar su mai shekaru 14 a duniya”
Wata mata, Mariya Inusa, mai shekaru 35 a duniya, wadda mazauniyar kauyen Rafin-Makadi ce, a karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina, ta shigar da karar mijin ta Inusa Aliyu wajen ‘yan sanda, da laifin aikata fasikanci da ‘yar su mai shekaru 14.
Mariya ta tabbatar da wannan ta’asa da mijin ta yake aikatawa bayan da ta kama shi dumu-dumu a cikin laifi, inda ta garzaya wajen ‘yan sanda.
Ta bayyanawa ‘yan sanda cewa, daman ta jima ta na zargin wannan abu, amma gashi yau ta gani da idonta da dubu ta cika kuma kuma daman ance gani ya kori ji domin ya tabbatar ma ta da zargin da ta jima ta na yi.
Mariya ta kara samun tabbaci daga wajen ‘yar ta su bayan da ta titsiye ta akan sai ta fada mata a gaskiyar lamarain inda ita kuma ba ta boye ma ta komai ba.
Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah, ya tabbatar da cewa, Inusa yana nan a hannun su domin cigaba da bincike kafin su tura shi gaban alkali.
Inusa ya amsa laifin da ake tuhumar shi da shi, kuma ya ce wani dan duba ne ya ba shi wani lakani kuma idan bai aikata fasikanci da ‘yar shi ba to kuwa lakanin zai karye.