Labarai

Kotu ta tasa keyar matashin da yayi sanadiyar rasa kafar Fatima zuwa gidan gyara hali

Wata kotun majistare dake a Sakkwato ta tasa keyar Aliyu Sanusi Umar matashin da ake zargi da yin tuƙin ganganci da yayi sanadiyar rasa kafar ɗalibar makarantar Khalifa dake Sokoto Fatima.

Wannan dai ya biyo ne bayan karar da lauyan Fatima suka shigar a gaban kotu, da suke buƙatar kotun ta kwatowa Fatima hakkin ta daga wanda ake zargi da zama sillar rasa kafar ta.

Lauyan mai karar a zaman kotun na yau dai ya bukaci ta, data duba yuwar bada belin wanda ake zargin la’akari da tanadin sashe 157 da 161, na dokar jihar Sokoto na 2019 ta hanyar bada belin wanda ake zargin har zuwa karshen Shari’a tai.Gyaran hali

Sai dai bayan jin bahasin lauya mai shigar da ƙara da wanda ake akarar, alkalin kotun ta bayar da umarnin tasa keyar matashin zuwa gidan gyara hali har zuwa 29 ga watan Agustan nan domin cigaba da sauraron shari’ar.

Barrister Mansur Aliyu shine lauyan wacce ke karar, ya sheda Aminu Amanawa, cewa sun shigar da karar ne, domin nemawa Fatima hakkin ta daga wanda ake zargin.

“An shigar da ƙarar ne bisa laifukan yin tuƙin ganganci, dama tuƙi ba tare da lasisin tuƙi ba, to da aka shigar da ƙarar an bada shi Beli a lokacin saboda wata ƙil yana da gata ko shi ɗan manya ne, amma da ƙoƙarin Chief Majistara na babbar kotu, da sashen shari’a na hukumar CID, an tuhumeshi da laifuka, kuma munji dadin da kotu ta kaishi gidan yari inji lauyan.”

Duk kokari da mukayi domin jin tabakin lauyan dake kariyar wanda ake karar kan lamari yaci tura.

Daga Aminu Amanawa a Sakkwato.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button