Jiya nayi mafalkin Buhari ya rike hannuna mun shiga Aljannah, Sirajo Sa’idu Sokoto
Wani matashi dan asalin Jihar Sokoto kuma dan gani-kashenin Buhar, Sirajo Sa’idu Sokoto ya bayyana wani mafalki mai nan al’ajabi da yayi wanda ya janyo masa cece-kuce a Facebook.
A cewarsa, jiya ya kwanta bacci inda yayi mafalki da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.
Ya ce ya yi mafalkin ya shiga Aljanna tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma a cewarsa, Buharin ne ya rike hannunsa.ha
Kamar yadda yayi wallafar:
“Jiya na yi mafalkin Buhari ya rika hannuna mun shiga Aljannah.”
Ba wannan bane karon shi na farko da yayi makamanciyar wallafar ba, akwai lokacin da yayi addu’ar Allah ya tarwatsa shirin duk masu son juya wa Buhari baya.
Bayan kwanaki kadan ‘yan bindiga su ka je su ka yi garkuwa da ‘yan uwansa da yawa a kauyensu da ke Sokoto.
Bayan nan ne yayi wata wallafa inda yace ya bar shekar Buhari, sakamakon sace ‘yan uwansa da aka yi.
A wannan karon ma, mutane sun dinga caccakarsa. Ga wasu daga cikin tsokacin jama’a karkashin wallafar tashi:
Abba Salisu Kasco Tsanyawa yace:
“Aljannah ta duniya ko ta lahira????
Daga duniya har lahira wlh babu wata alfarma da wannan tsohon zeyimaka
Kaima rashin sanin darajar kai da ciwon kai yasa kake tunanin wani Dan Adam zai kama hanunka zuwa gidan aljannah.”
A Sadeeq Jibreel Abdullahi yace:
“Baka kula sosai bane hanyar wuta ce kuka bi.”
Yusuf Sai Ta’allah yace:
“Yadda kasa Buhari arai kadaura masa so da Annabi kake yi wa haka da shi za kai mafarki ka ga da ka more.”
Abdu Danyaro Wudil yace:
“Kai wato kana karya ta hadisin manzon Allah ko.ai tunda shugaba bane shi kafin ya shiga Aljanna sai Allah ya tambayeshi.”