Kannywood

Harkar fim a yanzu mun yi girman da za mu bar wa yara__Jarumi Shuaibu Lilisco

Daga Mukthar Yakubu

FITACCEN jarumin Kannywood Shu’aibu Idris (Lilisco) ya bayyana cewa shi a yanzu harkar fim ya bar wa na baya, sai dai ya riƙa fitowa a matsayin manya kuma ya zamo mai bada shawara ga matasa masu tasowa.

Lilisco, wanda ya ƙware a wajen koyar da rawa kafin ya ƙara haske a fagen fitowa a matsayin jarumi, ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da mujallar Fim ta yi da shi a matsayin sa na tsohon ɗan wasa da ya jima ana damawa da shi a cikin harkar.

Ya ce, “To mu a yanzu sai dai mu yi godiya ga Allah da ya sa mu ka samu kan mu a wannan lokacin da wasu abubuwa sai dai mu ga ana yi. Domin kuwa a baya mu ake kallo, kuma wasu abubuwan ma idan ba mu ne mu ka yi ba, to ba zai yiwu ba.

Ya ƙara da cewa: “A a wancan lokacin ka ga idan ana maganar rawa ta zamani da ta gargajiya, ai mu ne masu yi kuma mu ne masu koyar da ita. Shi ya sa a lokacin mu ake kallo, mu ne jaruman.

Karanta kuma Matan Kannywood ne matsalar masana’antar, inji dattijo Auwalu Marshall “Amma a yanzu fa? Wasu ake yayi, su ne su ke cin lokacin su. To, ka ga kowa da lokacin sa. Don haka a yanzu ko da za mu fito a fim sai dai a matsayin iyaye ko wani rol ɗin da ya dace da babban mutum, shi ya sa za ka ga a finafinan da na ke fitowa a yanzu na fi fitowa a jami’in tsaro ko wani ma’aikacin ofis.”Harkar fim a yanzu mun yi girman da za mu bar wa yara__Jarumi Shuaibu Lilisco

Dangane da yadda harkar fim ta ke a yanzu kuwa wajen rashin tsari, jaruɓin ya ce, “Ai duk wannan abin yawa ne ya jawo hakan, domin a wancan lokacin ba mu da yawa, sai ka ga idan darakta biyu su na aiki to sun ɗebe jaruman masana’antar da sauran masu aiki, sai ka ga babu kowa. Amma a yanzu idan darakta ashirin su na aiki lokaci guda idan ka zo sai ka ga kamar ma wasu ba su tafi aiki ba.

“To, don haka an yi yawa, dole a samu rashin tsari. Wannan kuma ya sa aka samu raunin shugabanci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button