Harin jirgin ƙasa: Boko Haram sun karya alƙawari duk da mun biya musu bukatunsu — Gwamnati
Fadar shugaban kasa ta ce wadanda suka sace fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna sun kasa sako mutanen da sukai garkuwa da su, duk da biyan bukatunsu da gwamnati ta yi.
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC a yau Juma’a.
A tuna cewa, Buhari, a wata ganawa da ya yi da iyalan wadanda abin ya shafa a jiya Alhamis, ya ba da tabbacin kokarin gwamnatin tarayya na ganin an sako sauran mutane 31 da ƴan ta’addan ke ci gaba da garkuwa da su.
Sai dai yayin da yake watsi da ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya ba ta yi wats hoɓɓasa wajen ganin an dawo da wadanda aka yi garkuwa da su ɗin ba, Shehu ya ce gwamnati ta biya bukatun da ƴann ta’addan su ka nema.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta saki matar shugaban ƴan ta’addan mai ɗauke da juna biyu kamar yadda aka bukata.
Ya kara da cewa an sako wa ‘yan ta’addan wasu ƴaƴan su da ke hannun gwamnati a Adamawa.
“Bayan mun sakar wa shugaban ƴan ta’addan matarsa da ƴaƴansa, ya kuma nemi a saki wasu yaransu a Adamawa.
“Sai gwamnati ta aika jirgin sama cikin dare, a ka debo yaran a ka kai musu, da fatan cewa za su saki sauran wadanda su ke riƙe da su kuma za su cika alkawari.
“Amma sai gashi kawai sun kuma sake sabuwar baukata ta biyan kudin fansa. Amma sai ka ji mutane na cewa wai gwamnati ba ta yi komai ba. Wannan ba daidai ba ne,” in ji shi.