Labarai

Dubun Masu Garkuwa Da Mutane Da Ɓarayin Motoci Ta Cika A Jihar Katsina

A yau din nan ne majiyarmu ta samu wani labari daga jaridar Rariya inda dubun masu barayi na ciki wanda sun shiga yanzu yanzu haka ana kan bincike domin gurfanar da su a gaban kotu

Rundunar Ƴan sandan Nijeriya reshen Jihar Katsina ra kama ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

A yau Laraba 31 ga watan Agusta rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta gabatar da mutane goma sha tara, ga manema labarai da ake zargi da laifuka daban-daban a faɗin jihar.

Da yake gabatar da jawabinsa ga manema labarai, Ƙwamishinan Ƴansandan jihar Katsina CP Idris Dauda Dabban ya bayyana, gungun ƴan fashi da makami da Ɓarayin Motoci da aka kamo daga jihohin Kano, Bauchi, Jos da kuma Katsina, kazalika kuma an gurfanar da masu garkuwa da mutane guda Bakwai daga ƙaramar hukumar Danja.

An samu motoci guda goma sha uku, da Rasiɗin mota da suke haɗawa na bogi da hatimin da suke bugawa Rasiɗan da sunan saida Motocin. Akwai sauran nau’ikan makamai da suka haɗa da Adduna Wuƙake da makullen Motoci daban-daban, da ma Lambobin Motoci daban-daban.

A wani samamen kuma da rundunar ƴansanda ta jihar Katsina ta gudanar a ranar sha Biyu 12 ga watan Agusta sun dira maɓoyar Ƴan bindiga a garin Babban Duhu dake ƙaramar hukumar Safana, inda suka isa maɓoyar masu garkuwa da mutane, suka samu bindiga AK47 Guda da alburusai. Rundunar ta ce tana nan tana tsananta bincike akan lamarin

Da yake ƙarin haske akan masu laifin kakakin Rundunar ƴansandan jihar Katsina SP Isah Gambo ya bayyana waɗanda ake zargin Ɗaya bayan ɗaya da kuma laifukan da ake zargin sun aikata, kuma wasunsu sun tabbatar da laifin nasu a gaban manema labarai.

GWAMNA MAI MALA NAKOWA: Ya Raba Shanu Da Garmar Noma Ga Manoma Dari Uku

Mai girma gwamnan Jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni (Chiroman Gujba ) ya kaddamar da raban shanu da garmar noma ga manoma dari uku da hamsin da shida yau a garin dukumari dake karamar hukumar damaturu a babban birnin jihar Yobe.

Gwamnatin Jihar Yobe karkashin jagoranci Hon. Mai Mala Buni ta dauki mutum biyu (2) a kowane gunduma (ward) na jihar Yobe domin su amfani da wannan tallafin.

Agaskiya mu al’ummar jihar yobe munyi dacen adalin shugaba, Mai Mala Buni yana matukar kokari ajahar yobe baki daya wannan tallafin al’ummar jihar gabadane zasuci gajiyar wannan tallafin.

Muna addu’a Allah ya karawa Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni, lafiya da kwanciyar hankali Allah yarabashi da sharrin mahassada, amin ya Allah.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button