Da ana biyan matan aure kuɗin aikin da suke yi da sun zama hamshaƙan attajirai -Jarumar fim
Jarumar a masana’antar fina-finai ta Nollywood, Mary Remmy Njoku, ta nuna adawar ta kan masu cewa wurin mata yana a ɗakin girki ne.
Jarumar ta kuma soki mutanen dake da irin wannan tunanin na cewa mata a ɗakin girki aka san su, a wani rubutu da tayi a shafin sada zumunta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Jarumar ta nuna cewa maza sun fi mata sabawa da ɗakin girki amma wanda ake samun kuɗi a ciki
Njoku wacce tayi nuni da cewa sama da kaso 78 na manyan masu dafa abinci na duniya maza ne, ta ƙara da cewa yakamata a fara jinjinawa matan aure domin da ace ana biyan su kuɗin aikace-aikacen da suke yi, da sun fi wasu shugabannin banki samun kuɗaɗe.
Ta kuma ƙara nuni da cewa maganar gaskiya itace maza sun fi mata sabawa da ɗakin girki amma ɗakin girkin da ake biya inda suka kyale mata da ɗakin girkin da ba a biya su kula da shi.
Jarumar ta rubuta a shafin Instagram ɗin ta cewa:
Yakamata mu koyi jinjinawa matan aure nagari. Domin da ace ana biyan su bisa dukkanin aiyukan da suke yi, da sun samu kuɗaɗe fiye da wasu shugabannin banki.
Jarumar na auren shahararren ɗan kasuwa
Mary Njoku na auren shahararren ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa gidan talabijin na iROKO TV, Jason Njoku, sananna ce akan matsayar ta ganin mata sun samu gaskiya, daidaito da mutuntawa. Shafin Labarunhausa na wallafa