Kannywood

Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya

Advertisment

Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da ‘Wata Yarinya’ ta bayyana babban burinta a rayuwa. Legit na ruwaito

A cewar matashiyar jarumar wacce take haifaffiyar yar MaiduguriMaiduguri burinta shine ta zama babbar attajira kuma yar kasuwa.

Ta ce za ta so duaceniya ta santa a wannan fage na kasuwanci ta yadda zai kai sunanta ya danne na mai kudin Afrika kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote.

Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya

Advertisment

Maimuna wata yarinya ta bayyana hakan ne a yayin wata da hira da tayi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga bakin mai ita’. An tambaye ta menene babban burinta a rayuwa nan gaba inda ta ce:

Ka san shi dan adam yana da buri a rayuwa. Burina shine a duniyarmu ta yanzu da muke cikinta Ubangiji Allah yasa mu gama da duniya lafiya, shine burin mutum na farko. Sannan kuma burin mutum ba zai wuce yayi aure ya samu zuri’a dayyiba ba a rayuwa, toh wannan ma ina da buri.

“Amman ni burina shine ina so na zama irin attajiran macen nan yar kasuwa. Wanda irin ace zan zo ma in danne Dangote a suna, sai ace Hajiya Maimuna wata yarinya. Ka ga kowa yana da burinsa amma ni ina so in zama attajirar yar kasuwa wanda duk duniya za ta san da ita.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button