Labarai

Bidiyon yadda Boko Haram sunka shigar da Fulanin Jeji a Ƙungiyar Boko Haram

Advertisment

Tsawon shekaru akayi watsi da fulanin jeji makiyaya, an barsu cikin duhun jahilci babu karatun addini balle na boko, an ki shiga jeji a kai musu da’awar Musulunci duk da suna ikrarin Musuluncin

Yau mun wayi gari makiyan Arewa makiyan Musulunci sun samu nasaran ribatar watsi da fulanin jeji da akayi, aka tura maciya amana suka ci zarafin fulanin jeji, suka rabasu da iyayensu akan idon su, yau sun dauki makami sun zama ‘yan ta’addan dole suna azabtar da kowa a cikin KasaBidiyon yadda Boko Haram sunka shigar da Fulanin Jeji a Ƙungiyar Boko Haram

Ku duba ku gani yadda Boko Haram suka samu nasaran hada kan fulanin jeji suka shigar da su ayyukan ta’addanci, ku saurari khudubar da ‘yan Boko Haram suke yiwa fulanin cikin harcen fulatanci, tabbas karfin Boko Haram ya bar jejin Sambisa da Tafkin Chadi ya dawo Arewa maso yamma sansanin masu garkuwa da mutane

Ya kamata kowa ya shiga taitayinsa, wannan matsala Billahi bakin bindiga da ruwan bama-bamai na jiragen yaki ba zai iya kawar da ita ba, sai an koma gidan jiya an gudanar da bincike na gaskiya, duk wanda ya san sirrin tsaron Kasarnan ya san abinda nake nufi, hakika wannan lamari mai ban tsoro ne
InnalilLahi wa inna ilaiHi raji’un!
Yaa Allah Ka bamu mafita na alheri.

Advertisment

Ga Bidiyon nan kasa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button