Hausa Musics
Bidiyon Wakar Batsa da Wata Yarinya tayi Ta Jawo ce-ce-ku-ce
Advertisment
Dole ta sa zanyi wannan takaitaccen rubutu tare da wannan bidiyo na wata yarinya da tayi wakar batsa domin ya zama hujja
Tunda dai waka yana daga cikin abinda yake isar da sako har zuwa kunnen yara kanana, to yau mun wayi gari ‘ya’yan asara suna wakokin batsa, don haka wannan barazana ne ga tarbiyya da ya kamata a dauki matakin gaggawa
Yanzu zakaji yaro ko yarinya ‘yan shekara uku da haihuwa suna rera wakokin mawakan hausa na zamani, ya zakaji idan ‘yarka karama ‘yar shekara 3 ta shigo gida tana wakar a cire mata wando kamar yadda wannan mawakiya take rerawa?
Don haka ya kamata a kafa dokokin waka a jihohin Arewa domin a dakile mawaka haihuwan asara da suke wakokin batsa
Allah Ya sauwake.
Ga bidiyon wakar nan.