Labarai

Bello Turji da Wasu Shugabanni Yan Bindiga sun Aje Makamai – Cewar Nasiha

Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bello Turji, Ya Rungumi Zaman Lafiya a Zamfara

Zamfara – Shahararren shugaban yan bindiga, Bello Turji, ya rungumin shirin zaman lafiya da gwamnatin jihar Zamfara ta zo da shi a wani ɓangaren koƙarin kawo karshen ayyukan yan bindiga a jihar. Jaridar Legit na ruwaito

Mataimakin gwamnan Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, shi ne ya bayyana haka a wurin wani taro kan tsaro da ƙunguyar Ɗaliban jami’ar Madinah suka shirya a Gusau, babban birnin jihar.

Bello Turji da Wasu Shugabanni Yan Bindiga sun Aje Makamai - Cewar Nasiha
Bello Turji da Wasu Shugabanni Yan Bindiga sun Aje Makamai – Cewar Nasiha

Sanata Nasiha ya yaba wa ƙasurgumin ɗan bindiga Turji bisa ɗaukar matakin aje makamansa, kamar yadda jaridar Channesl tv ta ruwaito

Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa Matakin Bello Turji ya taimaka wajen dawowar zaman lafiya a yankunan ƙananan hukumomi uku, waɗan da kafin haka sune sahun gaba a ta’addancin yan fashin daji a Zamfara.

A cewar Sanata Masiha, a mako biyar da suka gabata, ba’a sake jin ɗuriyar rikicin Fulani da Hausawa ba a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi.

Hakan ta faru ne sakamakon tattaunawar masalaha da zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu da basu ga maciji da juna a jihar, a bayaninsa.

Duba da haka ne mai girma gwamna Bello Matawalle ya yi tunanin ya dace a bi hanyoyi da dama, bai kamata ya tsaya a musayar wuta da bindigu ba ko yaƙi da kowane irin makamai tsakanin yan fashin daji da mutane.”

Mun zauna da tawagar yan bindiga Tara – Nasiha

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa kwamitin da gwamna ya naɗa kuma ya ɗora shi a matsayin shugaba ya zauna taron sulhu da ƙungiyoyin yan ta’adda Tara (9) a yankin Magami, Masarautar Ɗansadau, da Maru domin su daina kaiwa mutane hari.

“Wannan ne dalilin da yasa a watanni uku da suka wuce a Magami, ba’a ji yan bindiga sun kai hari ba sakamakon shirin zaman lafiya. Kwamiti ya gana da tawagar yan ta’adda Tara kuma sun faɗi damuwarsu.”

Sun ce Hausawa na kai musu farmaki suna cin zarafin matan su, suna kashe Fulani a hanyar komawa gida daga Kasuwa. Ba’a gina mana makaranta da yaran mu zasu rinka zuwa ba, shiyasa suke shiga fashi.”
– Nasiha

Abinda Turji ya koma yi a yanzu – Mataimakin Matawalle

Mataimakin gwamnan ya kara da cewa TurjiTurji, wanda ya zama ƙusa a shirin sulhu na gwamna Matawalle, ya komayaƙar yan ta’adda domin tabbatar da zaman lafiya ya samu gindin zama a jihar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button