An Zalunce Ni Sama Da Miliyan 1 da Sunan Za A Yi Mun Fim Ƙarkashin Kannywood
Labarin da majiyarmu ta samu daga jaridar dimokuraɗiyyar ta ruwaito cewa akwai wata sabuwa jaruma da anka laƙume ma kuɗi da niyar za’a yi mata fim amma babu labari.
Sabuwar jaruma a Masana’antar fina finan Hausa wato Kannywwod, Fa’iza Muhammad wadda ta shiga harkar a shekaru biyu (2) da suka gabata, ta bayyana irin wasa hankalin da aka yi mata wanda take jin ƙuna a duk lokacin da ta tuna da abinda ya faru.
Jarumar ta ce anyi mata wasa da hankali matuka, kuma an zalunce ta, ta hanyar karbe mata kudi da sunan za a yi mata fim amma ba a yi mata, aka yi watsi da ita, babu kudin babu fim.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da shigowar ta harkar fim.
Fa’iza Muhammad wadda ‘yar asalin Jihar Adamawa ce a garin Girei, ta ce ta yi aure tun a shekarar 2008 in da suka zauna da mijin ta tsawon shekaru 10 a Birnin jihar Edo, kuma sun samu yara 3 kafin daga bisani suka rabu, kuma daga baya Allah ya yi masa rasuwa.
Jarumar Ta ce ”A shekarar 2020 na dawo Kano da zama, kuma hakan ya ba ni damar shiga harkar fim, wadda daman can ina sha’awar ta tun ina qarama.”
To sai dai a cewar ta “Na dauka shiga harkar fim abu ne mai sauqi wanda daga ka zo, za ka fara, kuma duniya ta san ka, sai da na shigo na gane abin ba haka yake ba.”
”Saboda gaskiya na fuskanci matsaloli da dama, don ka san harkar a na da yawa yanzu, kuma a komai idan za ka yi in dai ba ka nutsu ba, ka karanci yadda abin yake, to za ka sha wahala, don ka ga da na zo a farko duk da dai ba a kama suna, akwai wanda ya ce zai yi mini fim na kawo kudi, na dauki kudi na ba shi naira 400,000, aka zo aka samu matsala ba a yi mini fim xin ba kuma babu kudin, kuma na yi ta bada kudi haka a kai a kai, in bada 200,000, in bada 300,000, in bada 400,000, haka dai na yi ta ba su kudi su na cinyewa, don gaskiya kudin da na kashe a banza wadanda na san ba su amfane ni ba sun fi miliyan xaya ba tare da na yi nasarar yin fim din ba.
Sai ga shi daga qarshe Aminu Bala Mailalle ya kira ya saka ni a fim din sa Sawun Giwa, wanda ni na fito a matsayin jaruma, wanda kuma zan iya cewa shi ne fim dina na farko, kuma ina fatan ya zame mini matakin nasarar da nake nema na zama babbar jaruma.
Saboda haka Ina godiya a gare shi, Aminu Bala Mailalle da ya ba ni wannan damar kasancewa a fim din sa Sawun Giwa.”
Buhari ya aike da sakon murna ga Bishop Kukah
Shugaba Buhari ya taya Bishop Kukah murnar cika shekara 70 a duniya da kuma yi masa fatan nisan kwana.
Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar a ranar Talata.
Ya yaba masa bisa irin gudunmawar da yake bayarwa a matsayinsa na malami kuma marubuci, mai sharhi kan batutwan da suka shafi Najeriya.