Kannywood
An Ɗaura Auren Mawaƙi Aliyu Nata Mai Waƙar ‘Aure Martaba’ A Birnin Katsina
Advertisment
A yau asabar ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe aka ɗaura auren fitaccen mawaƙin nan Aliyu Isah Nata da Amaryarsa Zainab Suleiman (Zee Fulani). An ɗaura auren ne a masallacin Ƙofar Durɓi dake cikin birnin Katsina.


Fitaccen matashin mawaƙin wanda waƙarsa ta shura mai suna “Aure Martaba”, wadda waƙar aure ce da ake ji a duk faɗin Najeriya da ma ƙasashen ƙetare.
Mawaƙin ya samu tarin masoya a wajen ɗaurin auren nasa, tin daga abokan sana’arsa ‘yan fim, mawaƙa, daraktoci, masu ɗaukar nauyin shirin fim, masu kiɗan waƙa, da masu ɗaukar faifan bidiyo na fim, da kuma manyan masu bashi ayyukan waƙoƙi.
Bayan kammala ɗaurin auren, mun zanta da Ango a kan shin ko ya taɓa aure, inda ya bayyana mana cewa wannan shi ne aurensa na farko.