Addini

Abinda yasa matasan yanzu ba’a dorasu akan Manufa mai kyau ba – Dr Muhd Sani Umar R/lemo

A wajen majalisin karatu ash sheikh prof Muhammad Sani Umar R lemo yana bayyani a wajen muhaddara na dauko wani usulubi da anka dora matsan mu yanzu wanda ba shine alkiblarda ya dace ba, malam yana cewa:

Amma a yau miyasa matasan mu suke ba kamar na can da baya ba,wanda wannan tambayar dukkanin kowa yasan amsar.

Matasan yanzu ba’a kokarin dorasu a kan alkifla akan manufa ,yanzu abinda ake kokari idan yaro ya taso ya zaiyi kudi “how to make money”, eh wannan shine duk misalan da za’a basu wane yayi kudi, wane yana dan shekara kaza ya samu dalla biliyan kaza, wane tun yana dan shekara nawa yayi abu ya samu dala kaza saboda haka ƙwaƙwalwarsa yana akan kuɗi.Abinda yasa matasan yanzu ba'a dorasu akan Manufa mai kyau ba - Dr Muhd Sani Umar R/lemo

” A neman kudin zai iya zama komai shiyasa wajen neman kuɗin wani ya zamo dan fashi wani kidinafa wani barawo da dai sauransu ,wannan ba’a nan ake dora mutum akan manufa ba, wannan yana daya daga cikin abinda ya karya mu, ya karya matasa tunanin madda me za’a samu,me za’a tara a duniya.

Malam ya kara da cewa yanzu hatta da harka karatun mu sai kaga ana nunawa kayi course kaza anfi samun kudi,kayi course kaza anfi samun aiki a ciki, mai irin wannan manufar taya zai gina al’umma tunanin kansa kawai yake yi shi ya za’a ya samo wani abu.

Idan mutum yana makaranta da yaga inda ake samun kudi sai ya bar karatun ya koma can sai yace daman dan me ake karatun dan a samu kudi saboda me zan ɓatawa kaina lokaci.

Sa’a nan abubuwa da zasu kara shagaltar da mu a yanzu kuma shine harka social media din nan wasu zaka dukka lokutansu sun ɓatasu a social media irin , YouTube, Instagram, Pinterest, Twitter, Facebook da sauransu wanda kullum nan yake ɓata lokacinsa.”

Ga Bidiyon shehin malamin nan ku saurara kuji.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button