Ɗaurin Shekara 2 ko 4 ne Hukuncin Soja ko Ɗan Sandar da ya bari matar sa ta saka Uniform ɗin shi
Wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare a Nigeria inda Jami’an Sojoji dana ‘Yan sanda sukan bawa matan su ko ‘yayan su Kakin su su saka suyi hoto dashi, to saidai tambayar itace doka ta yarda da hakan ? Kamar yadda Shehu Rahinat Na’Allah ya wallafa a shafinsa
Eh to, kamar yadda muka sani Kakin Sojoji dana Yan Sanda da sauran su abune mai matukar girma da muhimmanci a idon Nigeria kasancewar sa yana da alaƙa da tsaron ƙasa da kuma rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka ne Nigeria bata yi wasa dashi ba.
Malam Bahaushe yana cewa “Matar Soja ita ma Soja ce” a gaskiyar magana kam wannan ba haka bane, domin kuwa laifi ne a Nigeria ka bawa Matar ka Uniform ɗin ka ta saka, kai koda ma hula ne bama Complete ba, idan kuma har ka yarda ka bata to matakin farko dakai da ita ɗin za’a tuhumeku da laifin “Conspiracy”
Conspiracy shine mutum biyu ko sama da haka su haɗu kuma su yarda akan zasu aikata wani abu da doka ta haramta, kamar yadda yazo a Shari’ar da akayi tsakanin Babarinde & ORS V State (2013)LPERC-SC169/2012 Sannan za’a iya chajin ku da laifin Conspiracy bawai dole sai kun aikata laifin ba, koda agreement kukayi akan cewa zaka bata ta saka to za’a chajeku da laifin, duba Shari’ar da akayi tsakanin Kayode V State (2016) LPELR-SC 83/2012, don haka dakai da ita ɗin zaku sha ɗauri na Shekara biyu na laifin Conspiracy.
Dangane da haramcin saka kakin Kuma mu duba Criminal Code Sashi na 110 za muga ya bayyana cewa haramun ne, Sannan, sai mu koma mu duba Sashi na 79 na Criminal Law of Lagos State, 2011 za muga ya tanadi ɗaurin Shekara 2 ne kuma babu zaɓin tara ga duk wanda ya saka kakin Soja ko na Ɗan Sanda, Indai ba Gwamna ko Shugaban ƙasa ne ya bashi lasisin ya saka ba, don haka kunga anan ma tana da hukunci na ɗaurin Shekara 2 a gidan Kaso, idan aka haɗa Shekara 4 kenan jimilla.
Amma idan ba shine ya bata ba itane kawai ta ɗauka ta saka to ba za’a chajesu da laifin Conspiracy ba, saidai ita za’a chajeta da laifin saka kakin, dogaro da Sashi na 110 na Criminal Code.
Haka Shima Jami’in Ɗan Sanda ba’a yarda ya saka kakin Soja ba, sai idan zasuyi aiki tare da Sojojin, to anan an basu dama su saka.