Yanzu – Yanzu : Tinubu ya zaɓi Kashim Shettima a matsayin mataimaki
Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban ƙasa.
Tinubun ya bayyana haka ne ga ƴan jarida a garin Daura yayin wata ziyarar barka da Sallah da ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. BBCHausa na ruwaito
A kwanakin baya ne dai Tinubun ya ɗauki Ibrahim Masari a matsayin mataimaki duk da tun a lokacin ana ta ce-ce-ku-ce kan cewa na riƙo ne, kuma shi ma Masarin a yayin wata hira da BBC a kwanakin baya ya tabbatar da cewa a shirye yake ya bar kujerar idan aka samu wanda ya fi shi cancanta.
Tinubun ya bayyana cewa duk da bai tattauna wannan batu da Kashim Shettima ba amma ga shi ya bayyana wa ƴan jarida.
Haka ma jaridun Najeriya na ruwaito cewa shi da kansa Ibrahim Masari ya janye daga takarar da kansa a wata wasiƙa da ya aika wa Jam’iyyar APC a ranar Lahadi.
Kashim Shettima dai a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar yankin tsakiya na Jihar Borno.
Haka kuma Shettima ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APC.
Wane ne Kashim Shettima
Tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar tsakiyar Borno Kashim Shettima gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya daɗe yana jan zarensa a siyasa musamman a arewa maso gabas.
An haife tsohon ma’aikacin bankin a ranar 2 ga watan Satumbar 1966 kuma ya yi karatu a Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Ibadan.
Daga nan ne ya shiga kasuwanci da kuma aikin banki inda ya kai ƙololuwa a aikin bankin. Ya zama gwamnan Borno a 2011 inda ya gaji Ali Modu Sherrif haka kuma an sake zaɓarsa a 2015.
A zamanin mulkinsa ne kungiyar Boko Haram ta yi ƙarfi matuƙa a Jihar Borno da wasu sassan jihar, amma duk da rikicin da jiharsa ke fama da shi, hakan bai hana shi yi wa jama’ar jihar aiki ba.
Bayan ya sauka daga gwamna ne ya tafi Majalisar Dattawan Najeriya a matsayin Sanata mai wakiltar tsakiyar Borno.