Opportunity

Yadda Zaka Cike Sabon tallafin bashi daga Nirsal Microfinace

A yau nazo muku da wani sabon tallafin bashi wanda bankin Nirsal Microfinance ya dauki nawin bayarwa ga kananan da kuma matsakaitan yan kasuwa. Shafin Hikimatv na ruwaito

Shi de wannan bashin da nirsal zai bayar ya kasu kashi biyu kamar haka:
  1. NMFB FETTY CASH NOW NOW
  2. NMFB SME

NMFB FETTY CASH NOW NOW: Wannan shiri ne domin iyayen mu mata da kuma maza masu Kananan sana’oi Kamar haka:

  • Masu saida Kosai
  • Masu wankin takalmi
  • Masu saida Abinci
  • Masu Rake
  • Masu yankan farce
  • Masu dako
  • Masu Lemu da ayaba

NMFB SME: Wannan shiri ne na Small and Medium enterprises wato Kananu da Matsakaitan sana’oi Kamar haka:

  • Masu shago karami
  • Masu kasuwanci
  • Masu shaguna
  • Manoma da sauransu

Duk Mai bukatar wannan rance ya Sai ya garzaya Bankin Nirsal mafi kusa dashi domin su bude masa account dasu.

Dalilin bude account din shine: zasu samu bayanan ka kuma da zarar sun bude maka account din zasu saka maka kudin daka nema rance.

Amma ka sani shi wannan tallafin bashi ne kuma dole saika biya su kudinsu.

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button