Yadda wata mahaifiya ta rasa ranta a wurin kare ɗanta daga ‘yan bindiga a jihar Bauchi
Wata mata mai shekaru 52 mai suna Maryam Mohammed, wacce ‘yan bindiga suka halaka yayin da take kare ɗan ta, mutane da dama waɗanda suka san ta da kuma da yawa da suka ji labarin ta na yabawa matuƙa da bajintar ta. LH na wallafa
Mazaunan Sabon Gari, wani ƙauye a Pali cikin ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, na murnar bajintar da matar ta nuna.
Jaridar Daily Trust ta samo cewa matar tayi ta maza inda ta tunkari ‘yan bindigan waɗanda ke son ɗauke mata ɗa. Sun halaka ta amma ba su samu damar ɗauke yaron ba. Sai dai yaron ya samu raunuka inda aka kaishi asibiti aka duba shi.
Yayin da yake yin jaje ga mazaunan ƙauyen, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana Maryam a matsayin jaruma.
Yace mutuwarta ba zata tafi hakanan ba, inda ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ƙarrama ta yadda bajintar ta za ta zama abin koyi ga sauran mutane, musamman mata.
Da take bada labarin lamarin, ɗiyar Maryam, Halima, tace ‘yan bindigan sun kawo hari a ƙauyen su da yammacin ranar sannan suka yita harbe-harbe, kowa na jin tsoron tunkarar su saboda suna ɗauke da muggan makamai.
Sun iso gidan mu sannan suka fito da babban yayana, Yaya, inda suka yi ƙoƙarin tafiya da shi, amma mahaifiyata ta buɗe ƙofar ta, ta fito sannan ta riƙe shi inda taƙi rabuwa da shi. Ta nuna musu bajinta sosai. A cewar ta.
Ta ƙara da cewa mahaifiyarta ta ɗauko taɓarya daga ɗakin girki, inda ta bugi ɗaya daga cikin har ta ji masa rauni a hannu.
Mahaifiyata na da jarumta. Su 11 ne su ka shigo gidan mu. Sun yi ƙoƙarin harbin ɗan’uwana amma da ba suyi nasara ba, sai suka yanke shawarar tafiya da shi, amma mahaifiyata taƙi yarda. Abin takaici sun kashe ta sannan suka gudu.

Da yake magana da ‘yan jarida, ɗan na Maryam wanda ya bayar da sunan sa a matsayin Babawuro Dan’azumi Mohammed, yace ‘yan bindigan sun yi ƙoƙarin harbin shi amma harsashi baya masa komai.
Wasu daga cikin mazaunan Sabon Gari waɗanda su kayi magana da Daily Trust akan mutuwar Maryam Mohammed, sun ce jihar Bauchi da Najeriya sun yi asarar uwa ta musamman.
Mutum ce mai ban mamaki, mai kirki sosai. Ko da yaushe tana ƙoƙarin taimakon mutane duk lokacin da take da hali. ‘Ya’yanta sune komai a wurin ta. Tana matuƙar ƙaunar su sosai. Ta nuna wannan ƙaunar ta hanyar sadaukar da rayuwarta saboda ɗan ta ya rayu. Allah ya gafarta mata.