Yadda Na kashe yaron na cire masa Kai da idanuwa – Cewar wani Matashi
Rahotanni Daga Jahar Bauchi, Nigeria Sun Nuna Cewa, Wani Matashi Mai Kimanin Shekara 25, Ya Kashe Wani Yaro Tare Da Cire Masa Kai Harda Kwakule Masa Idanu. Matashin Ya Shaidawa Manema Labarai Cewa, Yayi Amfani Ne Da Sanda Mai Kauri Wajen Kashe Yaron. Sa’annan Kuma A Yayin Bayanin Nasa Yace, Yayi Hakan Ne Ba Don Komai Ba Sai Don Neman Asiri Da Wani Boka Yayi Masa Alkawarin Zai Bashi Idan Har Ya Kawo Kan Mutum Tare Da Idanu.
Ko Wane Irin Magani Yakeson Hadawa?
A Yayin Bayanin Nasa Yace, Yana Yawan Razana, Shiyasa Yaje Wajen Boka Domin Yayi Masa Maganin Razanar. Daga Nan Bokan Yace Zai Masa Magani Ta Yadda A Duk Lokacin Da Idan Ya Tsorata Kai Tsaye Zai Bace. A Gurguje Dai Matashin Neman Maganin Bata Yaje Nema A Wajen Bokan.
Haka Zalika Matashin Ya Shaidawa Manema Labarai Cewa, Yana Da Mata Harma Da Yara Biyu Wadanda Ya Haifa. Ya Kuma Kara Da Cewa Wannan Ba Halinsa Bane.
Bayani Daga Rundunar Yan Sandan CID Ta Jahar Bauchi A Yayin Bayyanawa Manema Labarai Gaskiyar Al’amarin Sunce:
Ga bidiyon nan yaron da yake bayyani
https://youtu.be/H4s8OmtlRfM
Yayiwa Yaron Wayo Ya Ja Shi Jeji, Daga Nan Kuwa Ya Bugeshi Da Sanda Har Lahira (Innanillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun). Daga Nan Yayi Amfani Da Wukarsa Ya Datse Kan Yaron Tare Da Idanu Kamar Yadda Matsafi Ya Umurcheshi. A Lokacin Da Aka Kamoshi An Samu Wuka A Tattare Dashi Da Lighter, Da Kuma Mp3. Sun Kuma Karkare Da Cewa Suna Nan Kara Zurfafa Bincike Don Gano Gaskiya Tare Da Binciko Duk Wani Mai Hannu A Cikin Al’amarin.
Via onlinegist