Labarai

‘Shugaba Buhari ne ya hana daukar ma’aikata a Najeriya’, in ji ɗan majalisa

Wani ɗan Majalisar Dokokin tarayya a Najeriya ya ce akwai guraben aikin gwamnatin tarayya sama da dubu ɗari da ashirin amma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya hana a cike su. Daily Nigerian na wallafa

Honorabul Sani Bala Tsanyawa, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Ayyukan gwamnati na Majalisar Wakilan Najeriya ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da BBC Hausa.

BBC Hausa ta rawaito cewa ɗan majalisar ya ce tun a shekarar 2019 ne Shugaba Buhari ya sanar wa majalisar dokoki ɗaukar matakin a lokacin da ya je zaurenta domin gabatar da kasafin kuɗi.

A cewarsa “Lokacin gabatar da kasafin kuɗi da (shugaban kasa) ya kawo wa majalisa, yake faɗa cewa ya dakatar da ɗaukan aiki a ‘mainstream civil service’ – wato ma’aikatan da ke a aiki a ma’aikatu na kwaryar aikin gwamnati.”

Ya ce tun da shugaban ƙasar ya sanya wannan haramci ba a ƙara ɗaukar aiki ba a irin waɗannan ma’aikatu.

Sai dai a cewarsa an bai wa wasu ma’aikatun gwamnatin damar daukar ma’aikata saboda dalilai masu ƙarfi.

Ma su garkuwa da ƴan makaranta za su ɗanɗana kuɗar su -- Buhari
President Muhammad Buhari

Bangarorin da aka yi wa rangwamen sun haɗa da na tsaro da lafiya – sakamakon barkewar annobar korona.

Ya kara da cewa “Daga shekara biyar a baya zuwa yau, bincikenmu ya nuna cewa ma’aikata dubu ɗari da talatin ne suka bar aiki.”

“Wasun su ko dai sun mutu, wasu kuma sun yi ritaya, wasu kuma sun samu wani aikin na daban sun bar na gwamnatin tarayya.”

Ya ce amma a tsawon waɗannan shekaru biyar bayan sanya haramcin, mutum dubu shidda da dari bakwai ne kacal gwamnatin tarayya ta ɗauka aiki.

Sannan ya ce duk da haka har yanzu yawan guraben na kara yawa saboda a kodayaushe akan samu ma’aikatan da ke mutuwa ko ajiye aiki, to amma har yanzu ba a cire wannan haramci ba.

Sai dai ya ce akwai wasu hukumomin da a wani lokaci sukan dauki ma’aikata, kamar babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar sadarwa ta kasa (NCC), amma ba a ma’aikatun kwaryar aikin gwamnati ba, waɗanda a turance ake kira ‘ministries’.

Sai dai kuma Sani Bala Tsanyawa ya ce sau da dama kwamitinsa ya gabatar da kudiri a zauren majalisar wakilai domin ganin an cire haramcin da aka sanya kan ɗaukar aikin amma lamarin ya ci tura.

Ya ce “Ni shugaban kula da harkokin gwamnati na majalisar tarayya tare da wasu mambobin majalisar mun kawo kuduri sau daya zuwa biyu kan cewa a ɗage haramcin ɗaukar aiki.”

Bala Tsanyawa ya ce majalisa ta yi kokarin ganin an kawar da haramcin ta hanyar kiran hukumar kula da ma’aikata ta tarayya da kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya domin bayar da bahasi.

A cewar sa hukumar kula da ma’aikata ta tarayya takan ce ba laifinta ba ne, domin babu mai ikon fitar da gurbin ɗaukar aiki a gwamnatin tarayya sai shugaban ma’aikata na gwamnatin tarayya.

Ita kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya takan ce ba laifinta ba ne domin shugaban kasa ne ya sa haramcin ɗaukar aikin, ba ita ba.

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsanancin matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa.

Kiyasi na hukumar kididdiga ta Najeriyar ya nuna cewa kashi 42.5 cikin ɗari na matasan kasar ba su da aikin yi.

Haka nan kuma kashi 21 cikin ɗari na matasan da suke aikin ba a biyan su albashin da ya taka kara ya karya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button