Jaruman Kannywood sun tara wa ƙungiyar AKAFA aƙalla naira miliyan ɗaya
ƊIMBIN ‘yan fim sun bayar da gudunmawar kuɗi domin ƙaddamarwa tare da rantsar da shugabannin sabuwar Ƙungiyar Jarumai Mata ta Kannywood, wato ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA).
Binciken da mujallar Fim ta yi ya gano cewa ‘yan fim ɗin sun tara wa ƙungiyar kuɗi da su ka kai aƙalla naira miliyan ɗaya.shafin fimmagazine na ruwaito
Babu mamaki da shugabar ƙungiyar, Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa’a), ta faɗa wa wakilin mu cewa za a yi taron da ba a taɓa gani ba a masana’antar.
To, an dai yi taron an kammala a jiya Asabar, 23 ga Yuli, 2022 a Kano.
A cikin waɗanda su ka bada gudunmawar har da maza biyu, wato Baban Chinedu da Dauda Kahutu (Rarara).
Duk da yake ba mu gano ko nawa ita amara, wato Rashida, ta bayar ba, mun samo jerin yawancin waɗanda su ka bada gudunmawar da ta kai jimillar N830,000, kamar haka:
Aisha Ahmed Idris (Aishatulhumaira) – 50,000
Matar Dauda Rarara – 50,000
Saratu Giɗaɗo (Daso) – 5,000
Halima Atete – 100,000
Sabira Mukhtar – 20,000
Samira ‘Yar Ficika – 5,000
Samha M. Inuwa – 10,000
Raihan Imam Ƙamshi – 20,000
Baban Chinedu – 20,000
Dauda Kahutu (Rarara) – 100,000
Hafsat Idris – 20,000
Mas’udah ‘Yar Agadas – 5,000
Sadiya Gyale – 20,000
A’ishatu Umar Mahuta – 5,000
Aina’u Ade Bello – 5,000
Rahama MK – 5,000
Muhibbat Abdulsalam – 10,000
Hajiya Zuby – 5,000
Sabuwar Salma ‘Kwana Casa’in’ – 20,000
Fauziyya Sani (Maikyau) – 50,000
Hauwa Waraka – 10,000
Sadiya Haruna – 50,000
Maryam Mohammed Ɗanfulani (Mashahama) – 20,000
Asma’u Sani – 20,000
Baba Saude – 5,000
Hadizan Saima – 10,000
Maimuna 13×13 – 5,000
Hadiza A. 13×13 – 10,000
Maryam Isah Ceetar – 50,000
Maijidda Bello Bayero (‘Khusufi’) – 10,000
Zahra’u Shata – 10,000
Sadiya Adam – 10,000
Jamila Gamdare – 5,000
Hadiza Gabon – 100,000