Gwamnatin Nijeriya za ta ƙara haraji kan kiran wayar salula
Nan ba da daɗewa ba ƴan Nijeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 a kan kiran wayar salula bayan da gwamnatin tarayya ke shirin aiwatar da ƙarin harajin kaso 5 na yin waya a ƙasar.
Ministar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da harajin kiran wayar salula a Nijeriya a jiya Alhamis a Abuja.Jaridar Daily Nigerian na ruwaito
Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC ce ta shirya taron.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa, za a ƙara kashi biyar cikin 100 ne a kan harajin kashi 7.5 cikin 100 da tuni aka ƙara a kan duk kiran wayar salula da s ka yi, VAT, a ƙasar nan.
Ahmed, wacce ta samu wakilcin mataimakin babban jami’in ma’aikatar, Frank Oshanipin, ta ce harajin na kashi 5 cikin 100 da ake shirin aiwatar wa yana cikin dokar kudi: 2020 amma ba a aiwatar da shi ba.
Ta ce an samu tsaikon aiwatar da shi ne sakamakon tuntuɓa da gwamnati ta ke yi da masu ruwa da tsaki.
Ta ƙara da cewa za a riƙa biyan harajin ne a kowane wata, ko kafin 21 ga kowane wata.