Kannywood

Bayan mutuwar aurenta, Rahama Hassan ta bi sahun Rahama Sadau

A yadda lamurra suke wakana, a cikin kaf masana’antar Kannywood babu wata jarumar da ta kai jaruma Rahama Sadau samun caccaka musamman kan yadda take wallafa hotuna da bidiyoyi wadanda take rabar maza, LH  ta ruwaito.

Ba anan ta tsaya ba, tana yin shiga wacce ke fitar da tsiraicinta, wanda saboda haka yanzu haka ko ta yi makamancin abubuwan nan mutane sun dena mamaki ko kuma surutai akai.

Sai dai rashin damuwa da cakuduwa da mazar da take yi yana da alaka da shiga cikin jaruman Nollywood wadanda yawancinsu ba hausawa bane kuma ba musulmai ba.

 

Sannan akasarinsu ba ‘yan arewa bane don haka basu dauki dafa mace a komai ba don al’adunsu ba su hana su yin hakan ba.

Bayyanar wasu hotuna na jaruma Rahama Hassan rungume da wasu jarumai da mawakan kudu ya dauki hankula, duba da yadda duk da haramcin hakan a addinance da kuma al’ada ta zage tana ta hotuna a cakude cikinsu.

An ganta rungume da jarumi Gentle Jack wanda aka fi dani da Vuga, da wasu kuma rungume da mawakin Zule Zuu a wani taron wata kungiyar da ke da’awar hadin kan Najeriya (AVCIN).

Jaruma Rahama Hasan ta yi matukar taka rawa a masana’antar Kannywood tun daga shekarar 2011 zuwa 2015, inda ta fito a fina-finai da dama kamar Birnin Masoya, Madubin Dubawa, Lamiraj, Wasan Maza, Zarar Bunu, Wata Rayuwa da sauransu.

Ta auri wani dan siyasa mai suna Usman Elkudan a shekarar 2017, wanda Allah ya yi ma auren mutuwa a shekarar nan inda aka fara ganinta a masana’antar.

Masoyan jarumar ba su ji dadin ganinta a yanayin ba, musamman bayan an gan ta a tawagar 13 times 13, sai dai ganinta da wadannan ‘yan kudun zai fi bata musu rai.

Muna fatan Ubangiji ya yafe mata tare da ganar da ita ya kuma sa ta kara samun wani mijin tayi aure. Ameen.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Hassan Ramat (@rahama_hassan_real)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button