Kannywood

Bani ce Ajalin Darakta Mustapha waye ba – Zee Zango

Babu Laifi Ko Hannu Na a Mutuwar Darakta Nura Mustapha Waye - Zee Zango

Advertisment

“Ba ni da kambun baka kuma ban yi wa darakta Nura Mustapha Waye fatan mutuwa ba” – Cewar Zainab Salisu (Zee Zango) wadda ta yi wa Marigayi bidiyo kamin rasuwar sa.

Matashiyar jarumar Kannywood da aka gani tare da marigayi darakta Nura Mustapha Waye a cikin wani bidiyo da ke yawo a shafukan Sada Zumunta na zamani ta fito ta kare kan ta daga zargin da mutane ke yi mata na kasancewa mai kambun baka sakamakon fatan mutuwa da ta yi wa marigayi daraktan a cikin wancan bidiyon in da ta ke cewa, za ta yi masa bidiyo don idan ya mutu ta ta samu na Posting.Bani ce Ajalin Darakta Mustapha waye ba - Zee Zango

A yayin ganawar jaruma Zainab Salisu wadda aka fi sani da Zee Zango da tashar NAGUDU TV, ta yi mana bayani dalla-dalla game da dangantakar ta da marigayin da kuma dalili da lokacin da ta yi wancan bidiyon. Domin kamar yadda ta bayyanawa wakilin mu yayin wata doguwar tattaunawa da ya yi da ita kan wannan lamarin da ya zamo mata ƙalubale mai girma a cikin al’umma, shi marigayin ne da kan shi ya nemi da su yi wannan bidiyon kamar yadda ta ke yin bidiyo da wasu mutanen ta na wallafawa a shafin ta na Instagram. In da ya nemi da su yi bidiyo wala’alla ko idan ya mutu sai ta wallafa.

Ga cikakkiyar yadda ganawar jarumar da tashar NAGUDU TV ta kasance

Advertisment

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button