Opportunity

Yadda Zaka Kare Whatsapp Dinka Daga Masu Kutse (Hackers)

Jama’a Assalamu Alaikum Warahamatullah Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv.

A yau nazo muku da wani darasi akan yadda zaku kare whatsapp dinku daga masu kwace wato hackers.

Kamar de yadda kuka sani akan yawan samun matsala na kwacewa mutun whatsapp dinsa, wanda kana amfani da abunka lokaci guda sai kaga an kwace maka shi, ta hanyar wasu dabaru da masu kwacen sukeyi.

 

Hanyoyin da sukebi suna da yawa, kode su kiraka a waya suyi maka dadin baki da karya harsu karbi otp code dinka kokuma wata hanyar ta dabam wacce zasu yaudareka daga karshe su kwace maka acc dinka na whatsapl.

Kwacewar ba shine abun damuwaba, abun damuwar shine idan sun kwace maka, zasubi abokanka ne na whatsapp su karbi kudi a wajensu, kokuma su dinga tura tallah na karya domin su rudi abokanka har su sanya kudi aciki ta yadda daga karshe za’a kwace musu kudin.

Yadda zaku hana a kwace muku whatsapp din shine:

Da farko ku shiga whatsapp din naku saiku shiga alamar Dot dinnan guda 3

 

Daga nan saika shiga Settings

 

Sannan saika shiga Account

Daga nan saika shiga Two-step Verification

Anan zata kawo maka inda zaka seta saika seta kasa password din da kakeso sannan kuma ka memeta sannan saika sanya email address dinka kuma ka sake maimaitashi.

Shikkenan daga nan ka gama.

Note: Duk lokacin da wani zai yi kokarin hawa maka whatsapp to zasu turo maka da wani code wanda dole saida wannan code din sannan za’a samu damar hawa whatsapp dinka, Dan haka saika kula karka yarda wani ya kiraka yayi maka wayo yace za a turo maka wasu numbobi, kaikuma ka dauka ka bashi da zarar ka bashi lambobin da aka turoma nan take zai kwace maka whatsapp dinka.

Via Hikimtv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button