AddiniLabarai

Yadda mai wankin mota yayi min fyaɗe sannan ya ɗirka min ciki -Yarinya ‘yar shekara 11

Wata yarinya ‘yar shekara 11 ta shaida wa kotun sauraron masu aikata laifukan fyaɗe da cin zarafi ta Ikeja, jihar Legas, yadda wani mai wankin mota Ezekiel Udoh, mai shekara 39, yayi mata fyade sannan ya ɗirka mata ciki. LH na wallafa

Jaridar The Punch ta samo cewa lamarin ya auku ne a yankin FESTAC Town, na jhar a shekarar 2020.

Jami’in ɗan sanda mai tuhuma, Z.A Dindi shine ya jagoranci yarinyar wurin bayar da shaidu.

Yarinyar ta bayyana yadda yayi mata fyaɗe

Da take labartawa kotu yadda lamarin ya auku, yarinyar tace wanda ake zargin yayi amfani da ita har sau biyu.

A karon farko da abin ya faru, tace aikenta yayi bayan ta dawo ya sanya ta kai masa saƙon ɗaki, inda yayi mata fyaɗe.

Ta bayyanawa kotu cewa:

Udoh ya aikeni na siyo masa wani abu, bayan na dawo, ya ce min na kai masa sama. Bayan na kai sai yace na sanya masa a ɗakin shi inda anan yayi amfani dani a karon farko. Yace idan na faɗawa wani sai ya kashe ni.

A lokacin da yayi amfani dani a karo na biyu, na ga jini yana fitowa ta gaba na. Bansan cewa ina ɗauke da ciki ba. Kakata ta tambayeni meyasa nake ƙiba na ce ban da masaniya.

Ta haifi ɗa namiji

Yarinyar wacce yanzu ta kai shekara 13 a duniya, ta haifi ɗa namiji wanda yanzu haka yake da shekara ɗaya da wata biyar a duniya.

An ɗage sauraron ƙarar har zuwa 29 ga watan Satumba, 2022.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button