Labarai

Yadda magidanci ya rasa ransa wurin hana ‘yan bindiga ɗauke matar sa mai juna biyu

Wani magidanci mai suna Auwal wanda bai daɗe da yin aure ba ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga, bayan yayi ƙoƙarin hana su tafiya da matar sa, wacce ke ɗauke da juna biyu.

A ranar da lamarin ya auku, tunda sassafe Auwal ya kai amaryar sa, Rabi’atu, sashin masu haihuwa a Masukwani domin yi mata gwaje-gwajen da su ka shafi juna biyu. Bayan sallar Isha’i, ɗan’uwan sa Rabi’u ya kawo masa ziyara tare da matarsa Aisha. Sun ɗauki lokacin suna tattaunawa akan lamuran rayuwa har zuwa lokacin da Rabi’u ya so komawa gida tare da matar sa.  jaridar LH na wallafa

‘Yan bindiga sun zagaye gidan ɗauke da makamai

Tafiyar su kenan ba da daɗewa ba, Auwal yana kwance akan tabarma a cikin ɗaki, matar sa na zaune a gefen sa, ba su ankare ba kawai sai ga wasu gungun ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane ɗauke da bindigu sun zagaye musu gida. Ba su harbi kofar shiga gidan ba saboda dare bai yi ba sosai.

Sun ba Auwal umurni amma yayi watsi da shi, sun yi barazanar ɗauke Auwal tare da matar sa, nan ma Auwal yace ba inda za su je. Auwal ya miƙe domin tare kofar shiga ɗakin, amma abin takaici sai su ka harbe shi a hannu.

Auwal ya ji rauni sosai a hannu inda kusan duk ƙasusuwan hannun sa sun karye. Sun yi ƙoƙarin tafiya da matar sa, amma ya tirje cewa ba inda za su je. Daga nan sai ‘yan bindigan su ka harbeshi a ciki har sau uku, nan take ya faɗi ƙasa cikin jini. Daga baya sai su ka tagi da matar shi.

A lokacin da lamarin yake aukuwa, ɗan’uwan Auwal, mai suna Barde, yana cikin ɗakin sa amma tsoro ya hana shi fitowa. Bayan Barde ya lura ‘yan bindigan sun tafi ya samu ya fito yana mai faɗin sun kashe Danlami (Auwal).

Daga nan Barde ya samu ya kira ‘yan’uwa. Sai dai, duk da halin da Auwal ya tsinci kan shi, Auwal yayi ta neman taimako yana cewa, “ku ɗaga ni” sun ɗauke min matata, ya cigaba da cewa ku ɗaga ni har zuwa lokacin da ya kasa furta komai.

Wannan shine yadda wani ɗan’uwan sa ya bayar da labarin ga jaridar Leadership kan yadda ‘yan ta’adda su ka halaka Auwal Isah, bayan sun ɗauke matar sa, wacce a lokacin take ɗauke da juna biyu a garin Jere kan hanyar Abuja-Kaduna cikin ƙaramar hukumar Kagarko, a daren ranar Juma’a.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button