Wata mata ‘yar Najeriya ta mayar da N14.9m da ta tsinta, an bata kyautar maƙudan kuɗaɗe
Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Vicky Umodu, wacce ke rayuwa a San Bernardino California, ta nuna tsantsar gaskiya bayan ta mayar da zunzurutun kuɗi har N14.9m, wanda ta tsinta a cikin kujera. Jaridar LH ta rahoto.
An kawo mata kujerun har gida
Wasu mutane masu son bayar da kujerun kyauta ne su ka kawo wa Umodu kujerun har gida.
Matar dai ta tare ne a cikin sabon gidan ta dake a California, inda take neman sababbin kayan ɗaki na siya a shafin Craigslists.
Ta samu cewa akwai wasu mutane dake son yin kyautar kayan ɗakin wani ɗan’uwan su da ya rasu. Sai kawai ta nemi da a kawo mata su. Bayan an kawo mata kujerun, yayin da take duba su, sai kawai taga maƙudan kuɗaɗe ajiye a ɗaya daga cikin su.
Matar ta bayyana yadda lamarin ya auku
Umodu ta bayyana cewa:
Ban daɗe da tarewa ba, sannan bani da komai a cikin gidan. Naji daɗi sosai, sai mu ka ɗauko su zuwa cikin gidan.
Ina cewa yaro na, zo nan zo nan, wannan kuɗi ne! dole na kira mutumin!
Sun nemi mutanen da su ka basu kujerun inda su ka mayar musu da kuɗaɗen.
Umodu tace:
Ubangiji yayi min komai ni da yara na. Suna raye cikin ƙoshin lafiya. Ina da jikoki gida uku, me kuma zan nemi a wajen ubangiji?
Bayan ta mayar da kuɗin, an bata kyautar N900,000 saboda gaskiyar ta.
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
lulusmooth ya rubuta:
Ni gaskiya sai na ajiye su kamar na shekara ɗaya a wuri na kafin na mayar da su.
@poshest_hope ya rubuta:
Haka yakamata. Ba kuɗin ta bane.
@gucci_tos ya rubuta:
Ta yaya za su ajiye makuɗan kuɗaɗen idan ba shiri bane.