Opportunity

Wata Dama: Yadda Zaka Samu Kyautar N500,000 daga Kungiyar AiD Fundation

Assalamu Alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka.

Kungiyar AID FUNDATION: a karkashin shirin We-You Pro Campaign project wanda kungiyar Action Aid Nigeria ke tallafawa, Tana kira ga matasa ko kungiya na ’yan Najeriya wadanda suke da sabbin dabarun da za su iya hada dimbin jama’a (musamman mata da matasa) a cikin al’ummarsu don A wayar da kan su da tallafa musu da kuma wayar musu dakai akan yin rijistar masu kada kuri’a (CVR) don shiga wannan takara da kuma samun kyautuka da tsabar kudi Naira dubu 500 gaba daya.

Duk wanda zai shiga wannan gasa dole ne yayi video wanda yake nuna ya tara matasa musamman maza da mata, yana fadakar dasu akan muhimmancin yin katin Zabe (CVR) da kuma amfaninsa.

Bayan yayi bidiyon sai ya sanyashi a dukkan kafofin sada zumunta kamar: Facebook, intagram, ko twitter, Sannan sai kayi Hash tag na wannan: #CVRYouthInnovate da kuma tagging na @aidfoundation.

Za a zaɓi mutane ko ƙungiyoyin da suka tattara tare da tallafawa mafi yawan jama’a don karɓar kyaututtukan su ranar Juma’a 30 ga Yuni 2022.

Domin Shiga wannan gasa saika shiga Link din da yake kasa

APPLY HERE NOW

Allah yasa a dace Amen.

Via Hikima

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button