Wata budurwa ‘yar ƙasar Saudiyya ta gano cewa ita namiji ce bayan shekara ashirin 20
Wata budurwa ‘yar ƙasar Saudiyya, mai suna Randa, ta shiga shekarun ta na girma ba tare da taga wata alamar balaga ba, kamar sauran ‘yan mata.
A sakamakon haka, sai ta garzaya ta tuntubi likita, inda bayan bincike yayi bincike, sai aka gano ashe ita namiji ce ba mace ba. Jaridar Lifeinsaudiarabia ta rahoto kamar yadda majiyarmu ta samu Jaridar LH na wallafa a shafinta
Lamarin ya auku ne bisa kuskuren likita
An shaida mata hakan ne, bayan ta shekara ashirin da haihuwa. A lokacin da aka haifeta, likitan asibitin ya yi kuskuren ayyana shi a matsayin mace.
Mazakutar sa ta ɗa namiji, ta ɓuya ne a cikin cikin sa, sannan kuma akwai wasu yan matsaloli a wajen da mazakutar take. A sakamakon haka, maimakon a yi zuzzurfan bincike, sai kawai aka ayyana shi a matsayin mace ne shi.
Su kuma dangin sa da basu san dawan garin ba, sai kawai suka rangada masa suna Randa.
Ya samu gagarumin sauyi a rayuwar sa
Duk wani abu da ya aiwatar a baya dole ne ya canja shi, tun daga kan kewaye, rayuwar yau da kullum, mutuntaka, dama huldar sa da dangi, sannan kuma za’a yi masa tiyata wacce wani likita zai yi masa a ƙasar Birtaniya.
Amma abin sosa rai a cikin labarin shine hukumar Saudiyya ta yi fatali da takardun sa na neman fita waje, a cewar Randa. Iyalan sa ma sun yi korafi ga tsohon Ministan lafiya na kasar, amma har yanzu babu wani mataki da su ka dauka.
Bugu da kari, mahaifin Randa ya nemi taimako daga asibitin da aka karɓi haihuwar Randa amma babu wani bayani.