Labarai

The Lady of Heaven: An hana nuna fim kan Nana Faɗima ‘yar Annabi bayan jawo ce-ce-ku-ce

Hukumomin fina-finan Morocco sun haramta fim din nan na Birtaniya mai suna Lady of Heaven da ke janyo ce-ce-ku-ce, bayan da majalisar koli ta addini ta kasar ta yi Allah-wadai da shi.

Fim din ya yi iƙirarin bayar da labarin Nana Fatima, ‘yar Annabi Muhammadu (S.A.W).

Majalisar ƙoli ta malamai ta ce fim din “karya ce tsagwaronta” kan hujjojin da suka tabbatar da gaskiyar addinin Bbchausa na ruwaito

An yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da fim din a Birtaniya, haka ma Masar da Pakistan da Iran da Iraki sun yi tir da shi.

Majalisar ta zargi fim din da “nuna bangarancin akida “tare da zargin ‘yan fim din da neman suna” kuma sun yi fim din ne domin tayar da husuma tare da “bata ran Musulmi, a cewar kafofin yaɗa labarai na kasar Morocco.

Editan harkokin addini na BBC, Aleem Maqbool, ya ce an soki yadda mutumin da ya shirya fim din wanda dan Shi’a ne kuma malamin adinin Musulunci, Yasser Al-Habib, ya bayyana fitattun mutane a farkon zuwan adinin Musulunci wadanda ake girmamawa, inda ya nuna cewa akwai kwatance tsakanin ayyukansu da kuma na kungiyar IS a Iraki.

Mashiryin fim din mai suna Malik Shlibak ya caccaki wadanda ke son a dakatar da fim din a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana shi a matsayin son zuciya, ya kuma ce idan ba sa son fim din kada su kalla a maimakon haramta shi.

Haka kuma, a baya ya ce ba dukkan Musulmi ne ke son a dakatar da fim din ba.

Sakamakon zanga-zangar da aka yi a wajen wasu gidajen sinima na Birtaniya, kungiyar masu sinima ta Burtaniya wato Cineworld ta soke nuna fim ɗin na Nana Fatima don “tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatanta da abokan cinikinsu”.

Wannan kuma ya janyo fushin mutane ciki har da wasu Musulmin da suka so ganin fim din.

Editan harkokin addini na BBC Aleem Maqbool ya ce, saboda wasu ‘yan tsiraru ne suka yi nasarar aiwatar da nufinsu ta hanyar haramta fim din bisa dalilai na sabo.

Rashin mutunta mutane masu daraja’

Fim din wanda aka saki a gidajen sinima na Birtaniya a ranar 3 ga watan Yuni, ya yi ikirarin bayar da labarin Nana Fatima, ‘yar Annabi Muhammadu (S.A.W.).

Wasu kungiyoyi sun soki yadda aka kwatanta Annabi Muhammadu (S.A.W.) – wanda ake kallonsa a matsayin cin mutunci a adinin Musulunci – da kuma yadda aka nuna manyan fitattun mutane da ake girmama su a farkon zuwan Musulunci.

Kungiyar masu sinima ta Birtaniya ta dakatar da fim din bayan an yi zanga-zanga a Bolton, da Birmingham da Sheffield.

A Bolton, mutum fiye da 100 ne suka yi zanga-zanga a wajen gidan sinima, in ji Bolton News.

A cikin wani saƙon imel da aka aike wa kungiyar ta Cineworld – wanda kafar yaɗa labarai ta Bolton News ta ruwaito – shugaban majalisar koli ta masallatan Bolton, Asif Patel, ya ce akwai “akidar bangaranci” a cikin fim ɗin kuma “ya yi hannun riga da labaran tarihi da kuma rashin mutunta mutane mafiya daraja a tarihin Musulunci”.

Kafar yaɗa labarai ta 5Pillas ta kuma yada wani hoto a dandalin Twitter na abin da ta ce ya nuna Musulmi 200 ne suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da fim din a wajen wani reshen ƙungiyar Cineworld da ke Birmingham a ranar Lahadi.

Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna wani manajan gidan sinima na Cineworld da ke Sheffield yana sanar da masu zanga-zangar cewa an soke nuna fim din, in ji Guardian.

Mista Shlibak ya soki matakin da Cineworld ta dauka na janye fim din, yana mai cewa “bayar da kai ne” ga bukatun masu zanga-zangar.

Ya shaida wa BBC cewa: “Yanzu za su ga cewa za su samu biyan bukata a duk lokacin da aka bata musu rai.”

Msita Shlibak ya kara da cewa akwai miliyoyin Musulmi a Birtaniya, kuma zanga-zangar da aka yi ba ta dace da ra’ayoyinsu ba.

“Ya kamata mu yi taka-tsan-tsan wajan ganin ba mu ba da kai ba, wato fada wa jama’a cewa mu masu hakuri ne da kowa da kowa, mun amince da ra’ayoyi da matsayi daban-daban kuma za mu iya samun sabani, amma bai kamata a shigo da maganar haramci ba.”

Sai dai ya ce zanga-zangar ba za ta yi tasiri ba wajen dakatar da fim din baki daya, yana mai cewa akawai “‘yan Birtaniya da dama da yanzu suka ji labarin fim din a karon farko kuma wannan abu ne mai kyau a wurinmu”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button