Labarai
Osinbajo ya fi dacewa da tallar da gurguru da askirim maimakon shugabanci, Kashim Shettima
Advertisment
Tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima wanda ke goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa ya bayyana ra’ayinsa dangane da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, LIB da LH na ruwaito.
A wata tattaunawa da Channels TV ta yi da shi, Shettima ya tsaya akan cewa Tinubu ya ci cancatar zama dan takarar APC na shugabancin kasa.

Yayin da aka gwada masa sauran ‘yan takara kamar Yemi Osinbajo, Shettima ya ce duk da dai mataimakin shugaban kasar abokinsa ne kuma mutumin kirki ne, “Mutanen kirki ba sa dacewa da shugabanci.”
Ya kara da cewa, ya fi dacewa mutanen kirki su dinga siyar da gurguru da askirim ne.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




