Labarai

Nayi mafarkin Allah ya Ginawa Tinubu katafaren Gida Mai Bene Hawa Dubu Saba’in A Gida Aljannah – Hajiya Sa’adatu

Wata ƴar fafutukar yayata manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinumbu, Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi ta labarta cewa a daren jiya ta kwanta barci ta yi mafarkin Allah ya ginawa TINUMBU wani makeken katafaren gida na alfarka a gidan Aljannah wanda tsayinsa ya kai bene hawa dubu saba’in saboda mulkin adalci da aka nuna mata ya yi bayan zamansa shugaban ƙasa na shekaru 8 a Nigeria. Shafin Dokin karfe tv na wallafa haka a shafinsu na facebook.

Senator kashim Shettima

Hajiya Sa’adatu ta bayyana haka ne ya yin wata tattaunawarta da kafar sadarwa ta Dokin Ƙarfe TV, “Haƙiƙa Allah ya nuna min wani katafaren gida a Aljannah an kuma nuna min

cewa na Tinumbu ne, haka zalila na kuma ga wasu fararen mutane jajawur cikin fararan kaya sun kewaye Tinumbu a gidan da na yi tambaya su waye waɗannan sai aka ce mun ai su Kashim Shettima da Ganduje ne, da na tambayi dalilin haɗuwarsu sai aka ce ai su ne waziransa a gidan duniya lokacin da ya ke shugaban ƙasa, kuma sun taimaka masa wajen magance matsalolin ƙasar”. Cewar ta.

Governor Ganduje

Dogon Bauchi ta cigaba da cewa a lokacin da Tinumbu ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Nageriya ya samu ƙasar matsaloli sun addabe ta, kamar matsalar tsaro da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi, amma ya na hawa ko shekara ba a yi ba ya magance matsalolin ƴan Nageriya su ke rayuwa kamar a Saudiyya wanda hakan shi ne silar samun wannan gida a Aljannah kamar yadda ta gani a mafarkin, Inji ta.

Me za ku ce?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button