Labarai

Muhimman Abubuwa Guda 10 Da Yakamata kusani Game da sabon Alƙalin Alƙalan Nijeriya

Advertisment

An rantsar da Mai shari’a Olukayode Arwoola a matsayin muƙaddashin babban jojin kasar, sakamakon murabus da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi. BBCHausa na ruwaito

Mai shari’a Tankon ya  yi murabus ne bisa dalili na rashin lafiya.

Mai shari’a  Olukayode Ariwoola shi ne ke bi wa babban jojin Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad  baya – kuma ya sha rantsuwa tare da  karɓar ragama a matsayin mukaddasshin babban jojin Najeriya sakamamakon murabus din Mai shari’a Tanko.

An wayi gari da labarin murabus din babban jojin Najeriyar, Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, musamman ma yadda ya mamaye kafafen yada labaran kasar da dama.

Advertisment

Mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai Isa Ahuraka ya tabbatar wa manema labarai, cewa tun a ranar Lahadi Mai shari’ar ya ajiye aikin nasa.

Wane ne sabon babban jojin?

 

Buhari da Ariwoola

  • Mai Shari’a Olukayode Ariwoola shi ne alkali mafi girman mukami bayan murabus din Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad.
  • Mai shari’a Olukayade Ariwoola, an haife shi ne a watan Agustan shekarar 1954, kuma ya yi alkalanci a kotun daukaka kara ta Najeriya, kafin ya samu daukaka zuwa kotun kolin kasar.
  • Babban Jojin ya fara karatunsa ne a ƙaraar hukumar Iseyin ta jihar Oyo daga 1959 zuwa 1967.
  • Ariwoola ya kammala digirinsa a fannin shari’a a Jami’ar Ife wacce ta zama Jami’ar Obafemi Awolowo a Ile Ife da ke Jihar Osun a 1980.
  • Ariwoola ɗan asalin jihar Oyo ne kuma ya shafe kusan shakara 11 a matsayin ɗaya daga cikin manyan alƙalan Kotun Ƙolin, bayan shigarsa cikinta a watan Nuwamban 2011.
  • Kafin ya zama alƙalin Kotun Ƙoli dai yana Kotun Ɗaukaka Ƙara ne a matsayin ɗaya daga cikin alƙalanta, sakamakon ƙarin girma da ya samu daga Babbar Kotun Jihar Oyon
  • A yanzu bayan rantsar da shi, ya zama baban jojin Najeriya na 18, kuma ga alama shi ne zai ja ragamar yanke hukuncin shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na 2023 idan har an samu ƙorafi bayan zaɓen.
  • Mai shari’a Ariwoola na ɗaya daga cin alkalai bakwai na Kotun Ƙoli da suka yanke hukunci kan ƙarar zaɓen shugaban ƙasa na 2019 da suka tabbatar da Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na biyu.
  • Sannan ya riƙe amtsayin alkali a Kotunan Ɗaukaka Ƙara na  Kaduna da Enugu da kuma Lagos.
  • Mai shari’a Ariwoola ya yi ƙarin karatuttuka da kuma kwasa-kwasai a ƙasashe daban-daban bayan Najeriya da suka haɗa da Birtaniya da Faransa da Amurka da Birtraniya da UAE.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button