Labarai

Mahaifin wata ‘yar TikTok ya rasa Ransa bayan ganin bidiyonta tana rawar wakar batsa

Wata ‘yar TikTok ta yi sanadiyyar ajalin mahaifinta bayan ya ga bidiyonta tana rawa da wakokin batsa da zage-zage a kafar. jaridar LH na wallafa

Ganin bidiyon nata ke da wuya, wanda dama shi malami ne na addini, ciwonsa ya tashi yace ga garinku.

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito bidiyon wani mutum yana bayani, ya ce wani malamin addini ne ya ga diyarsa tana rawar TikTok wanda hakan ya yi ajalinsa.

Kamar yadda mutumin ya bayyana, daya daga cikin daliban malamin ya dade yana ganin diyarsa tana rawar amma sai yana kokwanton idan diyar malamin ce.

Ya ci gaba da shaida cewa watarana ya ga yarinyar ta saki wani bidiyo na rashin kyautawa, sai ya dauka ya nunawa mahaifinta bayan sun gama karatu.

Ya bayyana cewa an nuna masa bidiyoyi fiye da hamsin na diyarsa wadanda take nuna tsiraicinta da kuma rashin tarbiyya.

Ya bayyana cewa bayan ya tsare diyar da matarsa akan yadda su ka ci amanarsa yayin da su ka yi cirko-cirko, ya yanke jiki ya fadi kasancewar yana da hawan jini.

Ya ce bayan ya yi kwanaki a asibiti ya mutu sanadiyyar wannan takaici da bakin cikin da diyarsa ta sanya sa a ciki.

Malam yace wasu zasu idan kayi musu nasiha sai suce ae wannan ba komai bane idan an girma za’a daina wanda wannan ba abu mai amfani bani tun da kurciya a daina.

Ya kara da cewa zaka babbar mace tana live ba dan kwali a kanta saboda kawai a samu view’s da likes musamman wai a samu gift.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button