Labarai

Kullum ina kwana da baƙin ciki da takaici kan mutanen da matsalar tsaro ta shafa -Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana baƙin cikin da yake fama da shi akan matsalolin tsaron da su ka addabi ƙasar nan. Jaridar Labarunhausa ta rahoto

Shugaba Buhari yayi jawabi ga ‘yan ƙasa

Shugaba Buhari, a wani jawabi da yayi wa ‘yan ƙasa wanda da aka watsa da safiyar yau domin tunawa da ranar dimokuraɗiyya, yace yana rayuwa kullum da baƙin ciki da takaici kan waɗanda ta’addanci ya ritsa da su.

Ranar dai ta bikin tunawa da zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga watan Yunin 1993 wanda marigayi Moshood Abiola, ya lashe amma gwamnatin soji ta janar Babangida ta soke.

Ina roƙon kowane ɗan ƙasa da ya bada haɗin kai ga jami’an tsaron mu ta hanyar kawo rahoton duk wani duk wasu da baa yarda da su ba ga hukumomi. Za mu samu ƙasa mai zaman lafiya ne kawai idan mun kare aukuwar laifi ba bayan an aikata laifin ba.

Ya bayyana halin ƙuncin da yake shiga a dalilin matsalar tsaro

A wannan muhimmiyar ranar, ina son mu saka duk waɗanda matsalar ta’addanci ta ritsa da su cikin addu’o’in mu. Ina rayuwa kullum da baƙin ciki da damuwa kan duk waɗanda ta’addanci da garkuwa da mutane ya ritsa da su. Ni da hukumomin tsaro mu na yin iyakar bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mun ƙubutar da wannan abin takaicin ya ritsa da  su cikin ƙoshin lafiya

Waɗanda su ka rasa rayukan su, zamu cigaba da nemawa iyalan su haƙƙin su a wajen masu aikata laifin. Wadanda kuma ke tsare a yanzu haka, ba zamu huta ba har sai sun samu ‘yanci, sannan mun hukunta waɗanda su ka ɗauke su. Idan mu ka haɗa kawunan mu, za muyi nasara akan waɗannan wakilan ta’addanci da zubar da jini.

Saura ƙiris mu magance matsalar tsaro a Najeriya, Shugaba Buhari

A wani labari na daban kuma, Shugaba Buhari yace matsalar tsaro ta kusa zama tarihi a Najeriya. Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a saƙon da ya aikewa ‘ƴan Najeriya domin bukukuwan Easter.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa lokacin bukukuwan Easter na bana ya sanya ‘yan Najeriya sun yarda da cewa matsalar tsaro da halin ɗar-ɗar da ake fama da shi a ƙasar nan ya kusa zama tarihi. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Shugaba Buhari bayyana hakan ne a ranar Alhamis a saƙon Easter na shekarar 2022 da ya aikewa ‘yan Najeriya

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button