Kotu ta aike da wata mata gidan yari bisa yaɗa bidiyon tsaraicin tsohon mijinta
Wata kotun majistare da ke zamanta a Ƙaramar Hukumar Minjibir a Jihar Kano ta tasa keyar wata mata ƴar shekara 22 zuwa gidan gyaran hali sakamakon yaɗa bidiyon tsiraici na tsohon mijinta a kafar WhatsApp.
Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa laifin ya saɓawa sashe na 392 na kundin laifuffuka.
Yayin da take mayar da martani kan tuhumar, matar da ake zargin, Nafisa Lawan, ta shaida wa kotun cewa ta sanya bidiyon ne a ɓangaren “status” kuma yadda tsohon mijinta ne kaɗai zai gani, don haka babu wanda ya kalli bidiyon sai shi.
Ta ce, “Kafin na saka bidiyon, na tabbatar na saita shi ta yadda shi kadai ne zai gani. Ban san yadda abin ya faru ba.”
Alkalin kotun, Salisu Haruna Danbatta, ya umurci wanda ya shigar da karar ya kawo bidiyon gaban kotu, da kuma wadanda suka kalli bidiyon, sannan ya ɗage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.