Labarai

Kisan Hanifa: Kotu za ta yanke hukunci ranar 28 ga Yuli

Aliyu Samba

Wata babbar kotun tarayya dake Kano ta sanya ranar 28 ga watan Yuli domin yanke hukunci kan wani Malamin makaranta Abdulmalik Tanko, da ake tuhuma da laifin kashe yarinya ‘yar shekara biyar.

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Tanko, Hashimu Isyaku, mai shekaru 37, da Fatima Musa, mai shekaru 26, a ranar 14 ga watan Fabreru da laifuka biyar, da suka hada da hada baki don aikata laifi, da yin garkuwa da mutane, kisa da kuma ɓoye gawa.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.

Mai shari’a Usman Na’abba, ya sanya ranar ne bayan da Lauya mai gabatar da ƙara da masu kariya sun amince da rubutaccen jawabin su na karshe.

Tun da farko, lauyan waɗanda ake kara, Mrs Hasiya Muhammad, a yayin da ta amince da rubutaccen jawabin ta na karshe mai kwanan wata da kuma shigar da kara a ranar 31 ga watan Mayu, ta roki kotun da ta duba wadanda ake kara tare da sallamar su.

“Muna kira ga kotu da ta dauki jawabin mu da aka rubuta a matsayin hujjar mu ta baka a wannan karar,” in ji ta.

Lauya mai shigar da kara, mataimakiyar darakta mai gabatar da kara (DPP) Rabi Ahmad, a cikin rubutaccen jawabinta na karshe mai kwanan wata da kuma shigar da kara a ranar 6 ga watan Yuni, ta roki kotun da ta yanke wa wadanda ake tuhuma uku hukunci bisa laifin da suka aikata.

Rabu Ahmad ta kara da cewa wanda ake kara na biyu (Isyaku) yana kan shari’a ne bisa laifin boye gawa wanda ya saɓa da sashe na 277 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin kisa a sashe na 274(b).

“Muna rokon kotu da ta lura da abinda ke cikin sheda abar nuni ta 12 (bayani na ikirari) na wanda ake kara na biyu cewa ya binne gawar Hanifa,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wadanda ake tuhumar sun rufe karar ne a ranar 10 ga watan Mayu tare da shaidu uku.

Shaidu masu kare wadanda ake tuhuma su uku ne.

NAN ta ruwaito cewa lauyan mai gabatar da kara a ranar 12 ga Afrilu, ya rufe karar da ake tuhumar wadanda ake tuhumar da shaidu tara tare da gabatar da shedu ababen nuni guda 14 don tabbatar da karar su.

Tanko, mamallakin makarantar koyar da ilimin yara ta Nobel kida a Kano, ana zarginsa da yin garkuwa da Hanifa, a ranar 4 ga watan Disamba, 2021, ya yi garkuwa da ita a gidansa da ke Tudun Murtala na kwanaki kafin ya kashe ta kuma ya binne ta a wani rami a ranar 10 ga Disamba. 2021.

Laifin, kamar yadda doka ta shimfiɗa, ya saba wa tanadin sashe na 97, 95 da 273, 274(b) da 277 na dokar kundin laifuffuka ta jihar Kano na 1991.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button