Labarai

Jarumin Fina-Finan Nollywood, Jim Iyke, Ya Musulunta

Fitaccen jarumin nan a masana’antar fina-finan Kudancin Najeriya ta Nollywood, Jim Iyke, ya karbi addinin Musulunci.

Rahotanni sun ce jarumin ya karbi Musuluncin ne ranar Laraba a Owerri, babban birnin Jihar Imo, a gaban Babban Limamin Jihar, Suleiman Yusuf Njoku. Aminiya na ruwaito

Wani shafin kungiyar da ke yada addinin a Jihar, mai suna Islamic Calling Family ya tabbatar da labarin da daren Laraba.

Shafin dai ya wallafa cewa, “Daga karshe dai abokin Babban Limamin Jihar Imo, James Ikechukwu Esomugha, wanda aka fi sani da Jim Iyke, jarumi a masana’antar Nollywood, ya karbi Kalma Shahada.

“Muna addu’ar Allah Ya tabbatar da dyga-dugansa a Musulunci,” inji kungiyar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button