In Ba Don Ni Ba Buhari Ba Zai Ci Zabe Ba A 2015 — Tinubu
Ya bayyana hakan ne a Masaukin Shugaban Kasa da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, lokacin da yake zantawa da daliget din APC a Jihar. ranar Alhamis.
Yayin ziyarar dai, Tinubu na tare da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da na Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima.
Ya ce wannan ne karo na farko da yake bayyana hakan a Ogun, wacce ita ce Jihar Osinbajo ta asali, kuma wanda yake gaba-gaba wajen fafatawa da shi a takarar.
Ya ce a lokacin, Buhari ya ba shi damar ya zama Mataimakin Shugaban Kasa, amma wasu suka tashi tsaye cewa lallai ba zai yiwu Musulmai biyu su tsaya takara ba.
A cewar Tinubu, hakan ce ta sa aka bukaci ya kawo sunan mutum uku don su maye gurbinsa, inda ya bayar da sunayen Yemi Kadoso da Wale Edun da kuma Yemi Osinbajo, inda ya ce daga baya suka dauki Osinbajon.
Ya kuma ce, “In ba don ni da na shiga gaba a filin daga ba, Buhari ba zai samu nasara ba. Ya yi takara a baya sau daya, sau biyu, sau uku, amma duk bai yi nasara ba. Karewa ma har cewa ya yi ba zai sake tsayawa ba.
“Amma na je har gidansa a Katsina na ce masa ya fito, zai ci, amma kada ya yi watsi da Yarabawa. Tun da aka ci zabe ba a ba ni Minista ba, ba a taba ba ni kwangila ba.
“Saboda haka, wannan lokacin na Yarabawa ne, lokacina ne,” inji Tinubu.