Kannywood

Hukumar DSS ta kama mawakin da yaci zarafin yan matan kannywood

HUKUMAR Tsaron Ƙasa (Directorate of State Security, DSS) shekaranjiya ta tsare wani mawaƙi mai suna Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani) na tsawo kwana ɗaya sakamakon ƙarar sa da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta kai mata kan cin mutuncin da ya yi wa matan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood a wata waƙa.fimmagazine na ruwaito

MOPPAN, a cikin wata takardar sanarwa da kakakin ta, Malam Al-Amin Ciroma, ya fitar a yau, wadda aka miƙa wa mujallar Fim, ta ce kai ƙarar ya biyo bayan ƙorafin da “wasu mata” su ka kai wa MOPPAN a kan mawaƙin.

MOPPAN ta ce: “Biyo bayan wani ƙorafi da wasu matan Kannywood su ka aike wa shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: ‘Ƙorafin Cin Zarafin Da Wani Mawaƙi Mai Suna Sufin Zamani’, a cikin takarda wadda tsohuwar jarumar fim Wasila Isma’il ta sanya wa hannu, a madadin matan Kannywood, matan na Kannywood sun koka game da  yadda mawaƙin ya fito da waƙar cewa matan fim ba sa daraja aure, ba sa zaman aure, saboda sun saba da rayuwar fim da su ke samun kuɗi. Hakan, a cewar su, ba daidai ba ne.

Matan sun bayyana cewa da dama a cikin su su na zaman lafiya a gidajen su, wasu kuma su na aure a ko da yaushe. Kuma sun ka koka cewa waƙar za ta iya tunzura mutane su tsani ‘yan matan na fim.

“Jin haka, MOPPAN, a cikin gaggawa, ta tsunduma cikin binciken ƙorafin, daga bisani ta rubuta wa hukumar DSS domin ta yi abin da ya dace.

“Bayan da MOPPAN ta aike wa hukumar ta DSS ne, hukumar ta yi nata ayyukan, kana ta nemo gami da cafke mawaƙin.”

Ƙungiyar ta ce a ranar Laraba, 22 ga Yuni, 2022 ne, hukumar ta kamo Sufin Zamani, kana kuma ta bayar da belin sa a jiya Alhamis, 23 ga Yuni, bisa waɗannan sharuɗɗa:

1. Zai yi bidiyo da odiyo na ban-haƙuri da kuma ƙaryata kan sa game da waƙar ɓatancin da ya yi.

2. Zai yi waƙa kishiyar wacce ya yi, wato ya yabi matan Kannywood, ya faɗi alherin su kuma ya nuna masu zaman aure ne.

3. Zai rubuta wa MOPPAN takardar ban-haƙuri.

4. Zai yi wa hukumar alƙawari a rubuce, wato ‘undertaking’, cewar ba zai ƙara yin ɓatanci ga duk wani ɗan fim ba.

5. Bayan ya yi wannan kuma hukumar DSS za ta yi masa hukuncin  da ya dace, domin ya yi musu ƙarya a farkon kamun da aka yi masa.

Ƙungiyar ta kammala da cewa: “Duk wannan ya biyo bayan amincewa da ya yi cewa ya aikata laifin.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Wasila Isma’il dai ita ce maiɗakin kakakin na MOPPAN, wato Al-Amin Ciroma.

Haka kuma mujallar ta fahimci cewa ba da yawun uwar ƙungiyar matan masana’antar (K-WAN) ta rubuta ƙorafin ba.

Via

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button