Labarai

Borno 2023: Kai ba kowa bane -Martanin Zulum ga ɗan takarar gwamnan PDP

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya roƙi magoya bayan sa da kada su tanka kan sukar gwamnatin sa da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Mohammed Ali Jajeri, yayi, yana mai cewa Jajerin ba kowa bane.

A wani rahoton da jaridar Premium Times da Labarunhausa na ruwaito  fitar ranar Alhamis, Jajeri ya zargi Zulum da tafiyar da gwamnatin sa bisa ɓangaranci inda ake ba ‘yan’uwa da abokan arziƙi kwangiloli.

Mai magana da yawun Zulum ya mayar da martani

Da yake mayar da martani kan lamarin, mai gana da yawun gwamnan, Isa Gusau, yace daga shi har maigidan sa ba wanda zai tanka kan kalaman da Jajeri yayi, inda ya bayyana shi a matsayin ‘ɗan takarar gwamnan da baa san da shi ba’

Isa Gusau yace magoya bayan gwamnan da kada su tanka kan kalaman ƙage da zarge-zargen da su ka fito daga bakin ɗan takarar da baa san da shi ba na jam’iyyar PDP a jihar Borno.

Kamar yadda na saba, bari na fara da nuna godiyar gwamna Zulum ga dukkanin ku masu amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata ayyukan cigaba na gwamnatin jihar nan. Lallai kun yarda da ƙoƙarin da Farfesa Zulum yake yi na farfaɗo da jihar Borno daga ƙangin da ya faɗa a dalilin ta’addancin da ya kwashe fiye da shekara 12.

Kamar yadda kuka gani, a cikin ‘yan kwanakin nan, wani ɗan takarar gwamna da baa san da shi ba na PDP a jihar Borno, ya fitar hirarraki daban-daban na siyasa inda yake sukar gwamna Zulum gabanin zuwan zaɓen gwamna na 2023.

Maganar gaskiya itace, ko a cikin ƙusoshin jam’iyyar PDP na Borno baa san da shi ba.

A cewar Isa Gusau

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button