Labarai

Bidiyon wani matashi da yayi wuff da wata tsohuwar baturiya ya ɗauki hankula

Wani matashi ya ɗauki hankulan mutane da dama a yanar gizo bayan ya bayyana masoyiyar sa wacce ta girme shi da shekaru da yawa..

Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa a cikin bidiyon wanda aka saka a shafin Tik Tok, matashin da masoyiyar ta sa an gan su a cikin shaukin ƙauna. A wani sashi na bidiyon kuma an nuna matar a cikin ɗakin girki cikin jindadi.

Wasu na kallon soyayyar ta su a matsayin wacce ba soyayyar gaskiya ba

Mutane da dama da su ka tofa albarkacin bakin su akan bidiyon, ba su yarda cewa matashin ya faɗa cikin wannan soyayyar tsakani da Allah ba, sai dai domin abinda zai iya samu daga gare ta.

Sai dai kuma, akwai wasu mutanen da su kayi musu fatan alkhairi a soyayyar ta su inda su ke cewa shekaru basu hana ayi soyayya a tsakanin masoya.

Ku kalli bidiyon a nan

Mutane sun tofa albarkacin bakin su akan bidiyon matashin da masoyiyar ta sa

Wisdom ya rubuta: “

Aniyar samun katin zama ɗan ƙasa.

Encarnia M ya rubuta:

Haka lamarin ya zama kawai, me yasa mutane ke jin cewa sai sun bayyana ra’ayoyin su masu kyau ko mara sa kyau?

Sonja Feyzi Rahimi ya rubuta:

Yin soyayya da kakar ka domin samun fasfo

ABOUBAKAR IZMAIL ya rubuta:

Kana kuwa jindaɗi da mamarka?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button