Bidiyon karuwa tana cin mutuncin kwastomanta akan ya ki biyanta N60,000
A wani guntun bidiyon da shafin Instablog9ja ta saki wata karuwa ta ci kwalar kwastomanta yayin da ta ce ya ki biyanta hakkinta, Labarunhausa na ruwaito.
Kamar yadda ta bayyana, ta yi masa ayyukan da ya dace ta yi masa amma ya tsere ya bar ta ba tare da biyanta ko sisi ba.
A bidiyon wanda aka ga matar ta damki mutumin, mutane sun taru don sasanta su da jin abinda ya hada su.
Anan ne ta ke bayani kamar haka:
“Wannan mutumin ya gayyace ni, ya yi akawarin biyana N60,000. Bayan ya yi duk abinda ze yi da ni ya tsere ta katanga ya bar ni.
“Ga shi nan na kama shi. Ka biya ni kudina kawai. Ka biya ni.”
Zaku iya shiga nan domin kallon bidiyon Video
Tsokacin jama’a karkashin wallafar
Wannan bidiyon ya dauki hankalin mutane inda LabarunHausa ta tsinto wasu daga cikin tsokacin jama’a karkashin wallafar:
Mark Bosompem Wiafe ya ce:
“Yanzu mata ba su da kunya.”
Harry Peter Ugene ya ce:
“Gaskiya mutane sun haukace. Ban yarda cewa akwai masu kai wa karuwai ziyara ba sai yanzu.”
Okoye Celestine ya ce:
“In biya N60,000 ga wannan matar da ke bidiyon nan. Ubangiji ya kyauta.”