Kannywood

Ban taɓa rubuta waka ko daya ba – Mahmud Nagudu

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

 

A wannan kashi na 102, BBC ta tattauna da fitaccen mawaki Mahmud Nagudu, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa.

Ahmed Muhammad abdulkadir wanda anka fi sani da Mahmud nagudu yace shi tun yana yaro irin dan shekara Goma yake rera wakokin larabawa da bai san ma’anarsu ba.

Ya kara da cewa na fara waka a kannywood 01/1/2002 wanda bai sake dawowa yayi waka ba sai shekarar 2005 inda yace shi baiyi wakoki sosai a KannyWood ba amma mutane ke ganin haka domin kuwa akwai wanda har ya kirani yace yana da wakokina sama da dari biyar wanda ni kuma nasan banyi wakoki haka ba.

A gaskiya babu wata waka ta da nasan na taba rubutawa a duk cikin wakokina sai dai kawai in shiga studio in rera wakar da nake so kuma da yarda Allah kaga ta tafi.

Zaku iya sauraren cikakkiyar hirar daga jaridar Bbchausa da sunkayi wannan hirar da shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button