Labarai

APC ta faɗa tarkon mu, dama Tinubu muke so ya yi nasara, zai fi mana saukin suntumawa da kasa – Dino

Sanata Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa zaɓen fidda gwani na APC ya kawo wa jam’iyyar PDP komai cikin ruwan sanyi. Jaridar Premium times na ruwaito

Dino ya ce ” Allah ya ƙarɓi addu’arsu domin Tinubu muke so ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na APC kuma yayi.

” Tinubu zai fi mana saukin suntumawa da ƙasa a zaɓen shugaban kasa a 2023. Tun kafin wasu su gama karin kumallo a wannan rana mun fara bukin samun nasara, wato Atiku ya lallasa shi.

Dino wanda ya rubuta a shafin sa ta Tiwita ya kara da cewa dama dai tarko ne suka ɗana wa APC kuma ta kama su.

Idan ba a manta ba, Bola Tinubu ne yayi nasara a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban kasa da aka kammala a ranar Laraba a Abuja.

Tinubu ya yi nasara akan ƴan takara sama da 13 wanda suka fafata da shi a zaɓen.

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya zo na biyu da kuriu sama da 300 sau kuma mayaimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya zo na uku da ƙuri’u 200 da ƴan kai.

Shugaban majalisar dattawa wanda aka yi wa ganin shine jam’iyyar ta ke goyon baya ya zo na hudu da ƙuri’u 157.

Gwamna Yahaya Bello ta samu kuri’u 48 sai kuma Rochas Okorocha da Pasto Tunde Bakare da ba su samu kuri’u ko ɗaya ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button