Labarai

An Zaba Sanata Shettima A Matsayin Mataimakin Tinubu, Wakilin APC NWC Ya Bayyana

LABARIN SIYASA- Akwai masu ruwa da tsaki a Arewa a ranar Litinin da ta gabata, sun zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, a matsayin mataimaki ga mai rike da madafun iko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu. Jaridar politics gest

Wata majiya ta shaida wa Daily Independent cewa masu ruwa da tsaki a yankin na ganin cewa tsohon gwamnan jihar Borno ya fi tsohon kakakin majalisar wakilai, Hon. Yakubu Dogara da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wadanda rahotanni suka ce sun shiga takarar.

Da yake magana da sharadin sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai, mamban kwamitin ayyuka na kasa (NWC) ya ce “bayan muka yi la’akari da tsanaki muka sasanta da Sanata Shettima. Zai ba mu kuri’un da muke bukata.”

Da yake tabbatar da rahoton, Dr Garus Gololo, jigo a jam’iyyar APC ya yaba da zaben Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu, inda ya kara da cewa “Shawarar NWC za ta taimaka wa jam’iyyar ta samu nasara a arewa.”

“Wannan ci gaban yana nufin kafin karfe 12 na dare ranar zabe, jam’iyyar APC za ta kada Atiku da sauran ’yan takarar adawa, hannu. Alama ce a sarari cewa za mu ci zabe a 2023. Babu abin da zai hana mu, insha Allahu.” Ya ci gaba da cewa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button